Ibrahim El-Zakzaky: Kotu ta saki jagoran IMN da matarsa Zeenat

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.
A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin a ranar Laraba daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.
"Kotun ta sallame su ne saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja," a cewarsa.
Wakilin BBC a Kaduna Yusuf Tijjani ya ce jim kaɗan bayan bayar da hukuncin ne aka fita da jagoran na ƙungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement in Nigeria (IMN) a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko 'yan jarida ba.

Barista Sadau ya ƙara da cewa kotu ta yi tsokaci kan cewa "ta yaya za a zargi mutum da aikata laifi a 2015 sannan kuma a tuhume shi da dokar da aka samar a 2017".
An gudanar da zaman shari'ar na ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Gideon Kurada a asirce yayin da aka hana kowa shiga farfajiyar kotun balle ma ɗaƙin da ake gudanar da ita.
Sai dai gwamnatin Kaduna ta ce za ta ɗaukaka ƙara.
Tun a shekarar 2015 ne aka kama Sheikh Zakzaky bayan mabiyansa sun yi arangama da dakarun sojan Najeriya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Mabiyan nasa sun sha hawa tituna domin neman a saki jagoransu, inda suka dinga yin arangama da jami'an tsaro musamman a Abuja, babban birnin ƙasar.
A watan Yunin 2020 wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci 'yan sandan su biya ƙungiyar IMN mabiya Shaikh Ibrahim El-zakzaky naira miliyan 15 saboda kisan mambobinta uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.
Gaskiya da adalci sun yi nasara a kan zalunci - IMN

Asalin hoton, Other
Ƙungiyar IMN ta mabiya Shi'a wadda Sheikh El-Zakzaky ke jagoranta ta bayyana hukuncin kotun da cewa "nasara ce a kan gwamnatin Najeriya".
Cikin wata sanarwa da kakakinta Ibrahim Musa ya aike wa BBC Hausa, IMN ta ce hukuncin ba iya Zakzakya da matarsa kaɗai ya wanke ba "har da dukkan 'ya'yan ƙungiyar IMN".
"Shari'ar ba wai su kaɗai da kuma sauran 'yan IMN ta wanke ba, tabbas nasara ce wadda haƙuri ya haifar yayin da gwamnatin Najeriya ke gallaza [mana]," a cewarsa.
Ya ƙara da cewa "gaskiya da adalci sun yi nasara a kan kama-karya da zalunci".
Tarihin abubuwan da suka faru da El-Zakzaky da mabiyansa tun bayan tsare shi
Yadda Shi'a take a Najeriya

Asalin hoton, AFP
- Yan Shi'a tsiraru ne a Najeriya, amma rahotanni na nuna cewa yawansu na karuwa
- Kungiyar IMN, wadda aka kafa a shekarun 1980, ita ce babbar kungiyar 'yan Shi'a wadda Ibraheem Zakzaky ke jagoranta
- Tana gudanar da makarantu da asibitocinta a wasu jihohin arewacin kasar
- Kungiyar tana da tarihin arangama da jami'an tsaro
- IMN tana samun goyon bayan Iran inda 'yan Shi'a suke da rinjaye, kuma 'yan kungiyar na yawan zuwa Iran karatu
- Kungiyar Boko Haram da ke ikirarin bin mazhabin Sunna tana kallon 'yan Shi'a a matsayin fandararru, kuma ta sha kai musu hari.



























