Zakzaky ya ce ya samu shanyewar barin jiki
Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce ya yi fama da shanyewar barin jiki
Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko ranar Asabar tun bayan da aka kama shi fiye da shekara biyu da suka wuce.
Sheikh El-Zakzaky ya ce ya yi fama da karamar shanyewar jikin ne a cikin makon jiya.
Malamin addinin ya bayyana ne a Abuja tare da mai dakinsa Zeenah wadda ake tsare da su tare.
Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun yi wa gidansa kawanya.
Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria fitar na dauke da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga 'yan jaridar.
Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El-Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau.
Ya kuma gode wa 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suke yi masa.
A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa malamin ya rasu.
Ga yadda ganawarsa ta kasance da 'yan jarida:
'Yan jarida: Barka da rana?
'Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?
Sheikh El-Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)
'Yan jarida: Wane hali kake ciki?
'Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma'a 5 ga watan Janairun bana
Sheikh Zakzaky: Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin ya yi sauki
'Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?
Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami'an tsaro sun bari na gana da likitan. Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki.
'Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.
Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu'o'inku.
'Yan jarida: Mun gode
Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

Asalin hoton, Pr NIGERIA












