Suhaila el-Zakzaky: Ina cikin ƙuncin rayuwa kan tsare mahaifana fiye da kwana 2,000

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Ina cikin ƙuncin tsare mahaifana har kwana 2,000 - Suhaila Zakzaky

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon hirar BBC da Suhaila Ibrahim:

Iyalan jagoran ƙungiyar Ƴan uwa Musulmi a Najeriya IMN, Malam Ibrahim el-Zakzaky sun nemi gwamnatin ƙasar ta sakar musu iyaye bayan da suka shafe fiye da kwana 2,000 a tsare a hannun hukumomi.

A wata hira da BBC Hausa, Suhaila Ibrahim el-Zakzaky, ta ce ba su da wani buri da ya wuce su ga an saki mahaifansu sun sake rayuwa da su.

A ranar Alhamis 3 ga watan Yunin 2021 ne Malam Ibrahim ya cika kwana 2,000 a hannun gwmanatin Najeriya, tun bayan kama shi da aka yi tare da matarsa a Disamba na 2015 a gidansa da ke Zaria a jihar Kaduna.

Tun daga wancan lokacin mabiyansa suke ta kira ga gwamnati da ta sake shi, musamman bayan bayar da belinsa da kotu ta yi.

"Babban fatanmu shi ne a sake su, tun da shi kansa laifin da aka ce an riƙe su a kai to an saki duk wani da ake tuhuma da shi, an ce saboda babu hujja.

"To don me kuma za a ci gaba da riƙe su da aka ce su suka sa a aikata laifin?" a cewar Suhaila.

Ta ƙara da cewa a yanzu ma an kai matakin da ba a barinsu su ga iyayens nasu akai-akai kamar a baya.

Sannan ta yi ikirarin har yanzu akwai raunuka na harbinsu da aka yi lokacin da aka je tsare su da ba su warke ba, "kuma ba a mayar da hankali wajen ba su kulawar da ta dace ba."

"Rayuwarmu (ƴaƴansu) cikin waɗannan kwanakin na tattare da tashin hankali da wahala saboda raba mutum da iyaye ba za a iya haɗuwa a lokacin da ake so ko nkulawa da su ba, abin tashin hankali ne.

"Balle su a irin yanayin da aka ɗauke su," ta ƙara da cewa.

Wannan layi ne

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Me ƙungiyar IMN ta ce bayan kwana 2,000 da tsare Zakzaky?

Ƙungiyar ta IMN a wata sanarwa da ta aike wa manema labarai ranar Talata 8 ga watan Yuni ma ta ce, bai kamata ƴan ƙasar da dama su yi gum da bakinsu kan kamen da gwamnatin Najeriya ta yi wa shugaban nasu ba.

Shugaban sashen yaɗa labaran IMN Malam Ibrahim Musa da ya sa hannu a sanarwar ya ce: "Muna ganin shirun da mafi yawan ƴan Najeriya suka yi kan rashin adalci da zaluncin da ak yi wa Sheikh Zakzaky a matsayin abu mafi rashin dacewa a tarihin ƙasar.

"Shirunsu kan wannan babban rashin adalcin ba shi da maraba da masu goyon bayan hakan Ya kamata ƴan Nakeriya su gane cewa idan ka yi shiru kan lamari na rashin adalci, to fa kana goyon bayan waɗanda suke zalinci ne," a cewar sanarwar.

Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam'ian tsaro a Zariya.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Najeriya ta bayar da izinin fita da Sheikh Zakzaky Indiya don neman magani, sai dai kwanansa uku kacal ya koma kasarsa yana mai zargin cewa ba a bar shi ya ga likitocinsa ba.

Wannan layi ne

Abin da ya faru da Zakzaky da mabiyansa cikin shekara hudu

Tarihin arangamar 'yan Shi'a da jami'an tsaro da zanga-zanga da kuma shari'ar da ake yi wa jagoran kungiyar Islamic Movement In Nigeria, Ibraheem Zakzaky.
  • 1980s
    Sheikh Ibrahim Zakzaky ne ya kafa Islamic Movement In Nigeria(IMN)
    News image
  • Yuli 25, 2014
    Rahotanni sun ce an sojojin sun kashe mabiyan El-zakzaky guda 35 lokacin tattakin ranar Qudus a Zariya da ke jihar Kaduna. Uku daga cikin wadanda aka kashe 'ya'yan Zakzaky ne.
    News image
  • Disamba 12, 2014
    Sojoji sun yi zargin daruruwan mabiyan Islamic Movement In Nigeria da tsare wa hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Burutai, hanya a kan titin Sokoto road da ke Zaria, inda sojoji suka yi zargin kungiyar da yunkurin kashe Buratai, duk da kungiyar ta musanta.
    News image
  • Disamba 12-13, 2014
    An zargi sojojin Najeriya da kashe 'yan Shi'a 300 kuma suka binne gawarwakinsu. Sojojin sun musanta.
    News image
  • Disamba 14, 2014
    -
    News image
  • Nuwamba 14, 2016
    An kashe 'yan Shi'a takwas da dan sanda guda yayin wata arangama a lokacin wani tatttaki a birnin Kano. 'Yan sanda sun hana 'yan Shi'a yin tattaki daga Kano zuwa Zaria domin halartar ranar Ashura.Majalisar Koli ta Musulmi(NSCIA) ta ziyarci Sheikh Zakzaky a Abuja.
    News image
  • Disamba 2, 2016
    Wata babbar kotu a Najeriya ta ba da umarnci hukumar SSS da ta saki Elzakzaky a cikin kwana 45.
    News image
  • Janairu 20, 2017
    Kotun ta ce idan ba a bi umarninta ba to za ta kama sifeto janar na 'yan sanda na wancan lokaci, Ibrahim Idris da ministan Shari'a, Abubakar Malami da Darakta Janar na SSS, Lawal Daura, da laifin rasahin girmama kotu kuma za su iya fuskantar zaman gidan kaso idan suka ci gaba da yin burus da umarnin na kotu na Disamba 2, 2016.
    News image
  • Janairu 7, 2018
    Jmai'an tsaro sun kashe dalibai guda biyu a lokacin zanga-zangar neman a saki Elzakzaky a Kaduna d ake arewacin Najeriya.Duk da umarnin da babbar kotun ta bayar da a saki Zakzaky, amma yana tsare a hannun SSS a wani boyayyen wuri. Gwamnati ta sha ikrarin cewa ba ta da hurumin sakin Zakzaky saboda shari'ar da ke masa tana hannun kotu a jihar Kaduna. Hakan ne ya sa mabiya IMN suka lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai an saki jagoran nasu ko da kuwa za su kare baki dayansu.
  • Janairu 13, 2018
    Shugaban IMN, Sheikh Zakzaky ya bayyana a karon farko tun bayan kama shi, inda ya ce ya yi fama da bugun jini maras tsanani a ranar 5 ga Janairu. Zakzaky wanda yake sanye da wani abun wuya ya ce a karon farko an bar shi ya ga likitocinsa bayan da ya nace.
  • Afrilu 16, 2018
    Yan sanda sun yi rikici da 'yan IMN a lokaci wata zanga-zangar neman sakin Zakzaky a dandalin Unity Fountain, Abuja inda aka kashe mutum daya sannan da dama suka jikkata.
  • Afrilu 23, 2018
    Yan Shi'a sun sake haduwa da fushin 'yan sanda lokacin wani tattaki zuwa hukumar kare hakkin dan adam. An kama 'yan IMN akalla 115.
  • Mayu 15, 2018
    An gurfanar da Elzakzaky da matarsa Zeenat a gaban mai shari'a, Gideon Kurada na babbar kotu da ke Kaduna bisa tuhume-tuhumen kisan kai da taro ba da izni ba da kuma tayar da zaune tsaye da dai sauransu. Gwamnatin jihar Kaduna ce ta shigar da karar.
    News image
  • Yili 11, 2018
    Kotu ta dage karar zuwa 2 ga Agusta 2018
  • Agusta 2, 2018
    Kotu ta dage bukatar Elzakzaky ta neman beli zuwa Oktoba 4, 2018
  • Oktoba 4, 2018
    Alkali ya sake dage sauraron bukatar bayar da belin Zakzaky zuwa Nuwamba 17, 2018.
  • Oktoba 27, 2018
    Mbaiya Zakzaky sun yi dandazo a gadar Zuba da ke Abuja. Sun yi taho-mu-gama da tawagar sojoji da ke daukar makamai, al'amarin da ya janyo kashe 'yan Shi'a guda uku.
  • Oktoba 29, 2018
    An sake samun arangama tsakanin 'yan Shi'a da sojoji da 'yan sanda. Sojojin sun fadi cewa an kashe 'yan Shi'a guda uku duk da cewa 'yan Shi'ar sun ce mutum kusan 50 sojojin suka kashe.
    News image
  • Oktoba 30, 2018
    Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 400 bisa tuhumar tayar da zaune tsaye a Abuja. Jmai'an tsaro sun zargin 'yan Shi'ar da mallakar bam din da ake yi fetir guda 31 da sauran muggan makamai. Sojoji sun ce mutum uku ne suka mutu amma IMN ta ce gwammai ne.
    News image
  • Nuwamba 17, 2018
    Kotu ta yi watsi da bukatar neman beli bisa dogaro da cewa babu wata sheda daga likitoci da ke nuna bukatar belin domin neman lafiya.
  • Disamba 7, 2018
    Daruruwan magoya bayan Zakzaky sun hau titunan Abuja suna zanga-zangar neman a saki jagoransu.
  • January 22, 2019
    Mai shari'a Gideon Kurada ya yanke cewa hukumar DSS ta ci gaba da tsare Zakzaky da mai dakinsa, Zeenat sannan a ba shi damar ganin likitoci.
    News image
  • Yuni 29, 2019
    Mai shari'a Kurada ya dage karar ba tare da sanya wata rana ba saboda zai shiga sahun alkalan kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a jihar Yobe.
  • Yuli 9, 2019
    Yan sanda da 'yan Shi'a sun sake taho mu-gama a wajen majalisar dokokin Najeriya. 'Yan sanda sun ce an harbi jami'ansu guda biyu a kafa sannan an jikkata wasu guda shida da duwatsu. 'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 40. Sai dai wani mamban kungiyar Abdullahi Muhammad Musa ya shaida wa Reuters cewa 'yan sanda sun bude musu wuta, inda suka kashe masu zanga-zanga biyu a lokacin da suke kokairn shiga majalisar dokoki cikin ruwan sanyi.
    News image
  • Yuli 10, 2019
    Yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki El-zakzaky kamar yadda kotuna da dama suka yi umarni.
    News image
  • Yuli 18, 2019
    Mai shari'a D.H Khobo ta jagoranci zaman sauraron bukatar neman beli wadda aka dage zuwa 29 ga Yuli 2019. Ta ce "Yana da muhimmanci a fahimci cewa gwamnatin tarayya ba ta da hannu a ci gaba da rike da Zakzaky kasancewar shari'ar da ake yi masa ta koma hannun jiha. Ba kasafai ake bayar da belin mutumin da ake zargi da kisa ba abin da ya sa Elzakzaky da mai dakinsa ke dogara da batun neman lafiya."
  • Yuli 22, 2019
    Mataimakin kwmaishinan 'yan sanda, Umar Umar da dan jaridar gidan talbijin na Channels, Precious Awolabi da wasu 'yan kungiyar IMN 11 sun rasa rayukansu a rikici tsakanin jami'an tsaro da 'yan Shia lokacin wata zanga-zanga a Abuja.
    News image
  • Yuli 26, 2019
    Gwamnati ta samu hukuncin babbar kotu a Abuja na haramta ayyukan 'yan Shi'a mabiya Zakzaky.
    News image
  • Yuli 29, 2019
    Mai shari'a Darius Khobo ta babbar kotun jihar Kaduna ta dage sauraron bukatar Zakzaky da mai dakinsa ta zuwa India neman magani zuwa 5 ga Agusta. Sheikh Zakzaky bai je kotun ba.
  • Yuli 31, 2019
    IMN ta sanar da dakatar da zanga-zanga domin bin wasu sabbin hanyoyin warware rikicin da kuma kai gwamnatin tarayya kara a kotu kan haramta ta.
Tarihi daga Azeezat Olaoluwa da Princess Abumere da Olawale Malomo.
Hakkin Mallaka na hoto: Getty Images.

Yadda Shi'a take a Najeriya

Mabiya Shi'a a Najeriya

Asalin hoton, AFP

  • Yan Shi'a tsiraru ne a Najeriya, amma rahotanni na nuna cewa yawansu na karuwa
  • Kungiyar IMN, wadda aka kafa a shekarun 1980, ita ce babbar kungiyar 'yan Shi'a wadda Ibraheem Zakzaky ke jagoranta
  • Tana gudanar da makarantu da asibitocinta a wasu jihohin arewacin kasar
  • Kungiyar tana da tarihin arangama da jami'an tsaro
  • IMN tana samun goyon bayan Iran inda 'yan Shi'a suke da rinjaye, kuma 'yan kungiyar na yawan zuwa Iran karatu
  • Kungiyar Boko Haram da ke ikirarin bin mazhabin Sunna tana kallon 'yan Shi'a a matsayin fandararru, kuma ta sha kai musu hari.
Wannan layi ne