Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rihanna ta nemi gafarar Musulmi saboda an yi amfani da Hadisi a tallan kayan ƙawarta
- Marubuci, Daga Nabihah Parkar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Minute
- Lokacin karatu: Minti 2
Rihanna ta nemi afuwa bayan an yi amfani da wata waƙa mai jawo ce-ce-ku-ce a bikin tallata kayan ƙawarta mai taken Savage X Fenty.
An yi ta sukarta a shafukan sada zumunta saboda an yi amfani da waƙar mai suna Doom ta mawaƙiya Coucou Chloe, wacce ke ɗauke da Hadisi.
Rihanna ta ce yin amfani da Hadisin "bai dace ba" kuma "ba da niyya aka yi ba amma kuskure ne da bai kamata a yi ba".
Hadisi na nufin duk wani kalami da Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ya furta.
Baya ga Al-Kur'ani, Hadisi shi ne abu mafi muhimmanci ga rayuwar Musulmi.
An yi amfani da Hadisin da ke magana a kan ranar Alƙiyama a waƙar.
Mawakiya Coucou Chloe ta nemi gafara, tana mai cewa ba ta san cewa waƙar na ɗauke da Hadisi ba.
'Akwai bukatar daukar karin Musulmi aiki'
A baya an yaba wa kamfanin kayan ƙawarta na Rihanna Fenty saboda yadda yake gudanar da kasuwancinsa.
Sai dai wasu da ke goyon bayan Musulmi sun bayyana bacin ransu kan yadda aka yi amfani da wakar lokacin da ake nuna tallan kayan bacci na mata a Amazon Prime ranar 2 ga watan Oktoba.
Hodhen Liaden, mai shekara 26, marubuciya kan kayan ƙawa ne a shafin intanet wadda ke son Rihanna da Fenty amma ta ce sanya Hadisin a tallan kayan kuskure ne.
Ta ce ta ji dadi saboda afuwar da Rihanna ta nema ko da yake ta kara da cewa akwai kamfanoni irin nata "su sanya ƙarin Musulmi da za su gano irin waɗannan abubuwa".
Hodhen ta sayi kaya daga kamfanin Fenty a baya amma ta ce abin da ya faru yanzu zai iya sauya tunaninta.
Ta ce watakila ba za ta yi amfani da wasu daga cikin kayan da kamfanin ya aika mata ba domin ta tallata a shafin intanet
"Ba na ji zan rika sayen kayayyakin ko kuma tallata su a shafina na Instagram. Ina da akwatu cike da kayan Fenty waɗanda aka aiko min domin na tallata amma yanzu ban san ba ko zan yi haka."
Ba Hodhen ce kawai ta hasala ba. Arooj Aftab wata marubuciya kan kayan ƙawa ce a shafin intanet wadda ta yi magana kan amfani sanya mutane daga bangarori daban-daban a irin wannan kamfani.
Da take hira da BBC Asian Network kafin Rihanna da Coucou Chloe su nemi gafara, ta ce: "Lokacin da na kalli bidiyon ban ji dadi ba.
"Wannan Hadisi ne kuma an sanya shi a wakar da aka nuna mata suna rawa sanye da kayan bacci.
"Musulunci addini ne mai daraja - [amma abin da aka nuna ya saɓa wa hakan]. Ina ganin kowanne Musulmi ba zai ji dadin wannan gatsali ba."