Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Senegal: Kungiyoyin musulmi ba sa maraba da Rihanna
Wata gamayyar kungiyoyin addinin musulunci da ke kasar Senegal ta ce ba ta amince da zuwan shahararriyar mawakiyar nan ta duniya wato Rihana kasar ba.
Gamayyar ta fitar fadi hakan ne a wani taro da ta kira ranar Alhamis gabanin zuwan da mawakiyar da za ta yi a ranar Juma'a.
Gamayyar mai kungiyoyin addini 30 ta zargi mawakiyar da "Kasancewa 'yar kungiyar asiri ta Freemason da Illuminati da kuma madigo.
A baya dai masu hulda da ita sun sha nesanta ta daga irin wadannan zarge-zarge.
Rihanna dai ta yi niyyar kai ziyara kasar Senegal ne a matsayinta na jakadiyar wata kungiyar kyautata fannin ilimi ta duniya.
Kungiyar dai tana son taimakawa da kudi ne don koyar da miliyoyin yara da matasa a kasashe masu tasowa.
Ministan harkokin cikin gida na Senegal ya ce zai tabbatar da cewa an samar da tsaro ga dukkan wadanda za su halarci taron.