WHO za ta binciki ma'aikatan agaji da ke cin zarafin mata a Congo

.

Asalin hoton, Thomson Reuters Foundation

Hukumar Lafiya Ta Duniya wato WHO, ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan zargin cin zarafin mata ta hanyar lalata da ma'aikatan agajinta ke yi waɗanda ke yaƙi da cutar Ebola a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Kusan mata 50 ne suke zargin jami'an WHO da wasu ma'aikatan agaji na wata ƙungiya, kamar yadda wani bincike da wasu kafofin watsa labarai biyu suka nuna.

Ana zarginsu da bai wa matan ƙwayoyi cikin lemu, da kuma yi musu kwanton ɓauna a asibitoci da kuma turasasa musu su yi lalata da su, inda har biyu daga cikin matan suka ɗauki ciki.

An fara zargin ne tun daga shekarar 2018 zuwa Maris ɗin shekarar nan.

Hukumar WHO ta ce za a gudanar da bincike matuƙa kan lamarin.

"Duk wanda aka kama da laifi kan wannan zargi, zai yaba wa aya zaƙinta, wanda hakan zai haɗa da korarsa daga aiki nan take," kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.

Sama da mutum 2,000 suka mutu bayan ɓarkewar Ebola a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Hukumar WHO, wadda ita ce kan gaba wurin yaƙi da wannan cuta, ta fito a watan Yunin 2020 ta bayyana cewa an shawo ƙarshen annobar.

Wa ake ganin kamar ya fi laifi a binciken da ake gudanarwa?

Akasarin zarge-zargen da ake yi na cin zarafi ta hanyar lalata maza ake yi wa su, daga ciki har da likitoci waɗanda ake zargi daga WHO suke.

Aƙalla mata 30 ne suka gabatar da kokensu game da su, kamar yadda kamfanonin dillancin labaran suka ruwaito.

Zargi na gaba da aka yi, mata takwas ne suka yi zargin kan wasu maza takwas waɗanda aka ce daga ma'aikatar lafiya ta Congo suke.

An ambato wasu hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya biyu da kuma ƙungiyoyin bayar da agaji huɗu a rahoton.

.

Asalin hoton, Thomson Reuters Foundation

Wasu daga cikin mazan da ake zargi sun fito ne daga Belgium da Burkina Faso da Canada da Faransa da Guinea-Conakry da Ivory Coast.

Da dama daga cikin mazan ba su saka kwaroron roba, kuma aƙalla mata biyu sun samu ciki sakamakon cin zarafin.

Me kuma matan suka ƙara cewa?

Wata mai share-share da goge-goge mai shekara 25 an ambato tana cewa wani likitan WHO ya kirata zuwa gidansa domin su tattauna kan batun ƙarin girma da za a yi mata.

"Sai ya rufe ƙofar ya bayyana mani: Akwai sharaɗi. Dole mu yi jima'i a yanzun nan'," kamar yadda matar ta bayyana.

"Sai ya fara tuɓe mini kaya. Sai na ja da baya amma sai ya sa ƙarfinsa ya tuɓe mini kaya. Sai na fara kuka ina ce masa ya bari....Sai ya ƙi bari. Sai na buɗe kofar na fita da gudu."

.

Asalin hoton, EPA

A wani lamarin kuma, wata mata mai shekara 32 wadda ta warke daga cutar Ebola ta bayyana wa kamfanonin dillancin labaran cewa an kira ta zuwa wani otel domin wayar mata da kai.

Da ta je, sai aka ba ta lemu. Ta bayyana cewa tunda ta sha lemun ba ta farfaɗo ba sai bayan sa'o'i kuma ita kaɗai a ɗakin otel ɗin, inda ta yi zargin cewa fyaɗe aka yi mata.

Saboda me ake yi wa matan haka?

Mata da dama sun bayyana cewa an tursasa musu su yi lalata a musayar ba su aiki.

Matan sun ce an zo an same su ne a wajen kantuna, da wuraren ɗaukar aiki da asibitoci inda ake saka sunayen wadanda suka samu nasara.

Kamfanonin dillancin labaran sun ambato wata mata na cewa "yadda maza ke neman lalata da mata ya zama wata sabuwar hanya ɗaya tilo na samun aiki".