Coronavirus: Shin me rashin jin ɗandano ko ƙamshi ke nufi?

woman smelling a cut lemon

Asalin hoton, Getty Images

Rashin jin ƙamshi ko wari da ke faruwa sanadin cutar korona ya bambanta daga yanayin da mai fama da mura zai ji, in ji masu bincike a Turai waɗanda suka yi nazari kan bayanan da suka samu daga marasa lafiya.

Lokacin da masu fama da cutar korona suka daina jin ƙamshi, lamarin na zuwa ne kwatsam kuma yana ta'azzara.

Sannan mafi yawa ba sa samun toshewa ko yoyon hanci - akasarin mutanen da ke da korona za su iya yin numfashi cikin sauƙi.

Wani abin kuma da ya bambanta su shi ne ainahin rasa ɗandano.

Ba wai ɗanɗanonsu ya samu matsala ba ne saboda sun daina jin ƙamshi ko wari, a cewar masu bincike a mujalla kan cututtukan da suka shafi hanci ta Rhinology.

Masu fama da cutar korona da suka rasa ɗanɗanonsu ba sa iya tantance ɗaci da daɗi.

Kwararru na zargin hakan na faruwa saboda annobar ta shafi jijiyoyin jikin mutum da suke da alaƙa da ƙamshi da ɗanɗano.

Alamomin cutar korona sun haɗa da:

  • Zazzabi
  • Tari ba ƙaƙƙautawa
  • Daina jin ƙamshi ko rasa ɗanɗano

Duk wanda ya nuna waɗannan alamomin ya kamata ya keɓe kansa sannan ya shirya zuwa a yi masa gwaji domin sanin ko yana ɗauke da cutar. Su ma 'yan uwansa sai su killace kansu domin hana yaɗuwar cutar.

Me rasa ɗanɗano ko jim ƙamshi ke nufi?

Mutane da dama sun ce akwai lokacin da suka tsinci kansu cikin yanayin daina jin ƙamshi ko wari ko ma ɗanɗanonsu.

A zantawar da BBC ta yi da wasu mutane a Abuja da Kano, sun tabbatar da cewa sun kasance cikin wannan yanayi sai dai ba dukkansu ba ne suka ga alamun zazzabi ko mura a tare da su.

A tsawon makwannin da suka ce sun kasance cikin yanayin, sun ce ba sa iya bambance ɗaci da zaƙi da tsami ko da yaji mutum ya sa a baki ba zai ji zafinsa ba - sannan kuma babu maganar jin ƙamshi ko wari.

Kan haka muka tuntubi Dakta Nasir Sani Gwarzo wani ƙwararren likita a Najeriya kuma masani kan cututtuka masu yaɗuwa don jin abin da rasa ɗanɗano ko ƙamshi ko wari ke nufi.

Ya ce a al'ada akwai cututtuka da dama da suke haddasa canjin yanayi a maƙogwaron mutum ko dadashinsa ko hancinsa yadda idan ciwon ya kama wannan wuri zai iya haddasa rashin jin ɗanɗano ko wari ko ƙamshi - wannan yakan faru ga cututtuka da dama musamman waɗanda suke da alaƙa da mura.

Ita ma cutar korona cuta ce wadda take dangin mura amma wadda ake kira korona yanzu (Covid-19) sabuwar korona ce da ta fito a 2019.

"Idan mutum ya fara jin alamun rashin ɗnɗano ko wari wannan yakan faru galibi a kashi kusan 25 cikin waɗanda suka kamu da cutar korona, za su ji sun fara samun wannan alama - ko dai a matsayin ita kaɗai ce alamar da za su ji har su warke ko kuma ita ce alamar farko da za su bayyana idan ciwon ya kankama.

Nose

Asalin hoton, Getty Images

Wasu idan ya kankama su kan warke bayan kwanaki, wasu sukan warke daɗe za su iya yin shekaru ma da ɗanɗanon da jin wari ko ƙamshi duk ya tafi amma yawanci ya kan dawo cikin ƙanƙnin lokaci," in ji ƙwararren likitan.

Ya shawarci jama'a su tabbata zun ziyarci likita a duk lokacin da suka ga alamun haka a tattare da su don gano ko suna ɗauke da korona ne ko kuma wani dalilin ne daban saboda a cewarsa, a yanayin da ake ciki na annobar korona, ana samun irin wannan matsala sosai a tsakanin mutanen da ke fama da cutar.

Wannan layi ne

Bincike kan jin ƙamshi ko wari

Jagoran binciken Farfesa Carl Philpott daga Jami'ar East Anglia ya gudanar da gwajin jin ƙamshi da ɗanɗano kan wasu mutum 30: 10 masu fama da cutar korona, wasu 10 kuma masu fama da mura sai ƙarin wasu 10 da suke cikin ƙoshin lafiya - ba su da alamun mura ko zazzaɓi.

Rashin jin ƙamshi shi ne babban abin da aka gano tare da marasa lafiyar da ke fama da korona. Ba sa iya tantance ƙamshi sannan ba sa iya bambance ɗaci ko daɗi kwata-kwata.

Farfesa Philpott - wanda ke aiki da ƙungiyar tallafa wa mutanen da suka rasa ƙamshi wadda aka kafa domin tallafa wa waɗanda suka rasa jin ƙamshi ko wari ko ɗanɗano - ya ce: "Da gaske ne akwai alamun da ke bambanta cutar korona da sauran cututtukan numfashi.

"Wannan abun birgewa ne ƙwarai saboda hakan na nufin za a iya amfani da ƙamshi ko ɗanɗano wajen banbance masu cutar korona da mutanen da ke fama da mura."

Ya ce mutane na iya yi wa kansu wannan gwajin a gida ta hanyar amfani da gahawa da tafarnuwa da lemon zaƙi ko lemon tsami da kuma sikari.

Ya jaddada cewa gwajin da ake yi a makwogaro da hanci har yanzu suna da mahimmanci idan mutum ya yi tunanin ya kamu da cutar korona.

gwajin cutar korona

Asalin hoton, EPA

Mutanen da suka warke daga korona na iya jin ɗanɗano ko ƙamshi cikin 'yan makwanni kaɗan da warkewarsu, a cewarsa.

Farfesa Andrew Lane wani ƙwararre ne kan matsalolin hanci a Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.

Ya ce shi da tawagarsa sun daɗe suna nazari kan samfurin da ake ɗauka daga hancin mutum domin gano yadda korona ke haddasa rashin jin ƙamshi sannan sun wallafa sakamakon bincikensu a mujallar European Respiratory.

Sun gano wasu sinadarai masu yawa waɗanda ake samunsu a wurin hanci kaɗai kuma su ke sa mutum ya ji ƙamshi ko wari.

Ana tunanin sinadarin da ake kira ACE-2 shi ne wajen da ke ba korona damar shiga ƙayar halittar da ke jikin mutum sannan ta haifar masa da cuta.

Hanci ɗaya ne daga cikin wuraren da Sars-Cov-2, ƙayar cutar da ke janyo Covid-19, ke shiga jikin mutum.

Farfesa Lane ya ce: "Za mu ƙar gudanar da wasu gwajin domin gano ko da gaske ne ƙayar cuta na amfani da ƙayooyin halitta wajen samun damar sa wa mutum cuta.

"Idan hakan ta faru, muna iya maganin ciwon ta amfani da wasu magunguna da za a sa ta hanci."

Karin labarai da za ku so ku karanta:

Wannan layi ne