Coronavirus: Masu cutar sun kai miliyan 30 a duniya

Asalin hoton, EPA
Adaddin mutanen da suka kamu da cutar korona a duniya ya zarta miliyan 30.
Alkalumman da jami'ar John Hopkins da ke Amurka ta bayar sun nuna cewa cutar ta kuma hallaka sama da mutum dubu dari tara da arba'in a duniya tun bayan bullarta a China bara.
Har yanzu kasashen Amurka da Indiya da Brazil ne cutar tafi shafa.
Alkalumman sun kuma nuna cewa ana samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar a makonnin baya bayan nan a kasashen nahiyar turai.
Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
Alamomin cutar coronavirus

Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.
Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.
Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.











