Coronavirus a Najeriya: Yadda cutar korona ta jawo ƙarancin abinci a Kano da Legas da Abuja

Abinci

Annobar Covid-19 ta ƙara assasa matsalar ƙarancin abinci a Lagos da Kano da Ribas da Abuja a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa, NBS.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sabon rahotan da ta samu kan tasirin annobar korona a jihohin Kano da Legas da Ribas da babban birnin tarayyar kasar Abuja.

Rahotan a cewar NBS, ƙarancin abinci ya kai wani matsayi a jihohin uku, amma a Jihar Ribas da Birnin Tarayya Abuja abin ya fi muni.

NBS ta ce kashi 72 cikin 100 na magidanta na ƙorafin cewa ba sa iya samar da wadatuwar abinci a gidajensu.

"Magidanta a waɗannan jihohi hudu ba sa iya ware ko sisi a matsayin kuɗin ajiya.

''Sannan suna karɓar bashin kuɗi domin biyan wasu buƙatun yau da kullum, wanda ke sake jefa su cikin matsanancin yanayin tattalin arziki da rage kuɗaɗen da suke adanawa domin gaba."

Wannan layi ne

Ƙarancin kuɗaɗen shiga

Yan Najeriya na koka wa da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa
Bayanan hoto, Yan Najeriya na koka wa da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa

Me rahoton ya ƙunsa?

Rahoton wanda yake kunshe da sakamakon rubu'i na biyu na shekara ta 2020 kan bincike ma'aikata, ya ambato cewa hada-hadar tattalin arziki da mutane ke yi a waɗannan jihohi hudu ya yi kasa tsakanin Yuni zuwa Yuli 2020 kafin zuwan korona.

Rahotan ya kuma ambato a Abuja a matsayin inda kudin shigar mutanen da ke aiki suka yi kasa da kusan kashi 14 cikin 100.

"Ko da wasu mutane sun dawo aiki, kudaden shigar su ba zai dawo daidai ba, yayin da kudaden ma'aikata a Kano da Ribas suka rungumi noma sannan masu kananan albashi a Legas suka mayar da hankali kan sana'o'i sama da rawar da suke takawa kafin annobar korona."

Hukumar tayi bayyani cewa rubu'i na biyu na binciken ma'aikata da aka wallafa a 2020 ita ce ta harhado su tsakanin 17 ga watan Yuli zuwa 8 ga wata Yuli 2020.

Rahotan dai ya ba da cikakkun bayanai kan halin da magidanta suka shiga sakamakon annobar Covid-19 a Jihohi Kano da Legas da Ribas da birnin Abuja.

Wannan layi ne

Karin bayyani

Tun bayan ɓullar annobar korona ake fargabar hali na matsi da tattalin arzikin kasashe musamman Najeriya za ta iya tsintar kanta.

Baya ga tattalin arzikin mutane hatta ɗaiɗaikun jama'a an yi hasashen za su shiga matsi, saboda koma bayan da za a fuskanta a kuɗin shiga.

Tuni dai tasirin annobar ya soma nuna wa a Najeriya sakamakon hauhawar firashi da tsadar kayan masarufi da abubuwa more rayuwa.

Ƙarancin abinci na zuwa ne yayinda masu karamin karfi ke kuka da yadda sayen abincin ma ke gaggara saboda tsada.

Annobar korona dai ita ce hujjar da ake dogaro ko bayyana wa a matsayin dalilin duk wani matsi da ake ciki a Najeiya.

Wannan layi ne

Wasu ƙarin labaran da zaku so karantawa