Ambaliyar ruwa ta janyowa manoma asarar biliyoyi a birnin Kebbi

Asalin hoton, KebbiGovt
Gwamnatin Kebbi ta ce manoman jihar sun yi asarar shinkafa da sauran amfanin gona, wadanda kudinsu ya kai fiye da naira biliyan daya sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta faru a sassa daban-daban na jihar.
Hukumomi sun ce ambaliyar ruwan ta mamaye dubban hektocin filayen noma da gidaje, abin da ya haifar da asarar dukiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Kebbi na daga cikin jihohin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zaɓa domin bunƙasa noman shinkafa a wani shiri da ta bullo da shi a shekarun baya.
Yanayin da wasu manoma suka fada a jihar ya munana, inda wasunsu ke ganin cewa ba su taɓa fuskantar matsala kwatan-kwacin wadda suka samu kansu cikinta ba a cikin wannan damina.
Zaidu Bala Kofa daya ne daga cikin manoman da wannan asara ta rutsa da su kuma ya ce rabonsu da ganin irin wanann amabaliyar tun a 2011.
"Rabommu da ganin irin wannan ambaliya tun 2011 saboda wannan fadama ba mu san yadda za mu kwatanta [girmanta] ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "fadamar ta taso daga ƙaramar hukumar Audi zuwa Argungu zuwa Birnin Kebbi zuwa Kalgo zuwa Bunza zuwa Ɗakin Gari zuwa Kokumesi zuwa Bagudu.
"Wannan gaskiya ba ƙaramar asara ba ce."
Sauran mutanen da suka rasa albarkatun gonarsu a wannan bala'i sun koka ga gwamnatin jiha da ta tarayya.
Attahiru Maccido, shi ne kwamishinan aikin gona na jihar, ya ce duk da cewa hasashe ya nuna cewa ambaliyar za ta ci gaba da barna har zuwa wani lokaci, suna shirin bayar da tallafi a gwamnatance.
"Da ya ke tun kafin yanzu muna da masaniya, ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta tara dukkanin ma'aikatu domin ganin yadda za a bai wa mutane agaji," a cewar kwamishinan.
Noma musamman na shinkafa, na daga cikin manyan abin dogaro ga al'ummar jihar ta Kebbi tun bayan hawan gwamnati mai-ci ƙarƙashin shugaban Muhammadu Buhari, wanda ya kudiri aniyar farfado da bangaren noma bayan rufe kan iyakokin kasar.
Sai dai hadura irin wadannan ka iya mayar da hannun agogo baya ganin irin dinbin asarar da wannan ambaliya ta haifar ga manoman yankin.












