Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta raba mutane da gidajensu a Jamhuriyar Nijar

Nijar

Unguwanni da dama a birnin Niamey na Nijar sun wayi gari tsamo-tsamo cikin ruwa ranar Talata bayan wani ruwan sama kamar da bakin ƙarya da ya haddasa ambaliya daga Kogin Isa.

Ambaliyar ruwa ta yi awan gaba da gonaki da rusa dimbin gidaje
Bayanan hoto, Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gonaki da rusa dimbin gidaje

Ruwan sama da aka ringa yi kamar da bakin ƙwarya a 'yan kwanakin nan ne suka haddasa ambaliyar ruwan a babban birnin na jamhuriyar Nijar.

Ambaliyar ta rusa daruruwan gidaje da gadoji da dama gami da shafe gonakin shinkafa.

Jamhuriyar Nijar

Da dama daga mazauna birnin da suka kai miliyan daya da rabi suna zaune ne a gaɓar kogin na Isa.

Gwamnati ta yi kira ga jama'ar da ke bakin gaba da su ƙauracewa wajen, domin tsira da rayukansu.

Jamhuriyar Nijar
Bayanan hoto, Yadda wasu mata ke tsaye suna kallon yadda ruwa ya malale gidajensu

Wasu da ruwan ya tilastawa barin gidajensu sun ce sun shiga cikin mummunan tashin hankali kuma suna cikin mawuyacin hali.

Wata mata da BBC ta yi hira da ita ta ce ruwan ya rusa gidansu baki daya, kuma ba su samu diban kaya ba sai kadan.

Jamhuriyar Nijar
Bayanan hoto, Ambaliyar ta yi sanadi rayuka hudu

Unguwar Gaweye na ɗaya daga cikin inda ruwan ya fi yi wa ɓarna, inda gidaje suka rushe tare da malale hanyoyi.

Kuma mazauna unguwar da sauran sassan da lamrin ya shafa na samun mafaka a wasu wuraren daban.

Jamhuriyar Nijar

Faraministan ƙasar ya ce ambaliyar ruwan ta zo musu ba zata.

Amma ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen datse ruwan da ya ke tahowa daga wasu ƙasashe maƙota.

Jamhuriyar Nijar
Jamhuriyar Nijar
Jamhuriyar Nijar