Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta raba mutane da gidajensu a Jamhuriyar Nijar

Unguwanni da dama a birnin Niamey na Nijar sun wayi gari tsamo-tsamo cikin ruwa ranar Talata bayan wani ruwan sama kamar da bakin ƙarya da ya haddasa ambaliya daga Kogin Isa.

Ruwan sama da aka ringa yi kamar da bakin ƙwarya a 'yan kwanakin nan ne suka haddasa ambaliyar ruwan a babban birnin na jamhuriyar Nijar.

Ambaliyar ta rusa daruruwan gidaje da gadoji da dama gami da shafe gonakin shinkafa.

Da dama daga mazauna birnin da suka kai miliyan daya da rabi suna zaune ne a gaɓar kogin na Isa.

Gwamnati ta yi kira ga jama'ar da ke bakin gaba da su ƙauracewa wajen, domin tsira da rayukansu.

Wasu da ruwan ya tilastawa barin gidajensu sun ce sun shiga cikin mummunan tashin hankali kuma suna cikin mawuyacin hali.

Wata mata da BBC ta yi hira da ita ta ce ruwan ya rusa gidansu baki daya, kuma ba su samu diban kaya ba sai kadan.

Unguwar Gaweye na ɗaya daga cikin inda ruwan ya fi yi wa ɓarna, inda gidaje suka rushe tare da malale hanyoyi.

Kuma mazauna unguwar da sauran sassan da lamrin ya shafa na samun mafaka a wasu wuraren daban.

Faraministan ƙasar ya ce ambaliyar ruwan ta zo musu ba zata.

Amma ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen datse ruwan da ya ke tahowa daga wasu ƙasashe maƙota.