Me ya sa iyaye a Najeriya ke garƙame 'ya'yansu?

Ana zargin mahaifin Ahmed Aminu da kulle shi tsawon shekara uku

Asalin hoton, HARUNA AYAGI

Bayanan hoto, Ana zargin mahaifin Ahmed Aminu da kulle shi tsawon shekara uku

Watan Agusta na 2020 na cike da wani sabon juyin na kubutar da mutane a arewacin Najeriya, kwatankwacin wanda aka fuskanta a karshen shekarar da ta gabata inda aka ringa kubutar da daruruwan mutane daga gidajen mari.

A wannan karon, 'yan sanda da kungiyoyin kare hakkin bil adama ne suka dukufa wajen kubutar da mutanen da iyalensu suka kulle su, a cikin mummunan yanayi.

Lamarin ya fara ne a watan Satumbar 2019 yayin da 'yan sanda suka gano wani gidan gyaran tarbiyya ko kuma gidan mari a garin Kaduna ba tare da sahalewar hukuma ba, inda aka sanyawa wasunsu mari. Kusan mutum 500 ne aka kubutar a jihohi biyar.

To amma a 2020 lamarin ya sauya daga wuraren da ake tsare mutane da dama, zuwa gano inda iyalai suke kulle 'ya'yansu a gidaje ba tare da kulawar da ta kamata ba.

Mutanen da aka kubutar a watan Agusta

'Yan sanda sun kubutar da brahim Lawan bayan shekara biyar a kulle. Yan sanda sun kama mahaifinsa bisa zargin cin zarafinsa.

Asalin hoton, Others

  • 12 ga Agusta: 'Yan sanda sun kubutar da wani yaro Jubril Aliyu mai shekara 10 wanda ake zargin mahaifinsa da daure shi a turken dabbobi
  • 14 ga Agusta: 'Yan sanda sun ceto Ahmad Aminu mai shekara 30 bayan tsare shi tsawon shekara uku
  • 20 ga Agusta: 'Yan sanda a Kano suka kubutar da wani wani mutum mai shekara 55, wanda danginsa suka tsare shi tsawon shekara 30 saboda matsalar kwakwalwa
  • 20 ga Agusta: Salisu Muhammad mai shekara 45 da 'yan sanda suka kubutar a Sokoto. Rahotannin sun ce dan uwan mahaifinsa ne ake zargi ya tsare shi har tsawon shrkara 25. Danginsa sun ce yana fama da matsalar kwakwalwa.

Halin da aka samu mafi yawan mutuanen dai yana da tayar da hankali. Da damansu a dakin suke ba fita ko ina tsawon shekaru, a nan suke kashi da fitsari, a nan suke rayuwa cikin kazanta da yanayi mai ta da hankali.

Tuni dai 'yan sanda suka tsare iyaye ko dangi na kusa na mutane da aka kulle a gida, domin amsa tambayoyin da kuma gurfanarwa gaban kotu, yayin da su kuma mutanen da aka tserar ke samun kulawar likitoci.

Jama'a da dama dai na ganin cewa baya ga wadannan, za a iya samun mutane da dama da danginsu suka tsare su a gida, wasu a cikin mawuyacin hali, tare da hana musu duk wani 'yanci na walwala.

Ana zargin mahaifin Jubril Aliyu da tsare shi a birnin Kebbi

Asalin hoton, @KBSTGOV

Bayanan hoto, Ana zargin mahaifin Jubril Aliyu da tsare shi a birnin Kebbi

Me ya sa iyaye ke kulle 'ya'yansu?

Faruwar lamuran dai suna taso da tambayoyi da dama kan dalilan da za su sa iyaye su kulle 'ya'yan cikinsu a cikin irin wannan mawuyacin hali.

Iyaye ko dangi na fakewa da matsalar kwakwalwa ko kuma shaye-shaye a matsayin dalilan da suke sa iyaye na tsare 'ya'yan nasu, to sai dai wasu na ganin sam wannan ba dalili ba ne na ci musu zarafi.

Wani masanin zamantakewa a Jami'ar Usman Danfodiyo Sokoto Dokta Usman Abdulkadir ya ce, mafi yawan mutanen ake tsarewa suna zaune ne ba tare da iyayensu mata ba.

"Suna zama ne da matan mahaifansu, saboda rabuwar aure ko kuma mutuwa."

Ya ce "a mafi yawan lokaci, ko da uban yana gida, mata ne ke kula da abubuwan da suke faruwa a gidan, kuma da wuya iyaye maza su iya magana."

Masanin bai amince da masu cewa ana tsare mutanen don gyaran tarbiyya ba, ko kuma saboda a yi musu maganin matsalar kwakwalwa ba.

"Gidajen ba asibitoci ba ne, idan mutane suna fama da matsalar tabin hankali, akwai asibitoci da ya kamata a kai su domin samun kulawa.

''Dubi yaron da aka ceto a Kebbi, halayyarsa ta sauya ta sha banban da ta mutane. Cin zarafin bil adama ne," a cewar Dr. Usman.

Ya kara da cewa, mutane da dama suna yin aure ba tare da za su iya daukar nauyin da ya rataya a wuyansu ba, don haka ne suke gaza ba su kulawar da ta kamata wajen ciyarwa da samar da matsugunni.

Wannan layi ne

Shin gwamnati ta gaza ne?

Dokta Usman Abdulkadir ya ce gwamnati na da hannu a cikin wadannan matsaloli, saboda yadda ta mamaye komai, yayin da dukiya kadan take tafiya ga jama'ar da ake mulka.

Ya ce cin hanci da rashawa sun sa gwamnati ta gaza sauke nayin da ke kanta a fannin tattalin arziki da lafiya da ilimi da kuma noma.

Sannan hukumomi a duka matakai ba sa mai da hankali wajen samar da cibiyoyin kula da masu laluran kwakwalwa da ta gyaran tarbiyya kamar yadda ake bukata.

Wannan layi ne

Mafita

"Wajibi ne gwamnati ta tabbatar da cewa an samar da isassun cibiyoyin gyaran tarbiyya a duka matakai, a cewar Dokta Usman.

Masanin ya kara da cewa wajibi ne mutane su yi kyakkyawan tsari gabanin aure kan yadda za su kula da iyalensu. Hakan a cewarsa zai ba su damar bibiyar duk wani hali da iyalensu suke ciki, da kuma ba su kulawar da suke bukata.

Ya kuma ba da shawarar cewa wata hanyar kawo karshen matsalar ita ce idan makota sun lura da an kulle wani, to su kai rahoto ga hukumomi domin daukar matakan da suka kamata.