Kano: 'Yan sanda sun shiga neman mahaifin da ya tsare ɗansa shekara 15 a ɗaki

Wani mutum a Kano

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce an tsare Ibrahim Lawal a wani ɗaki tsawon shekara 15
Lokacin karatu: Minti 3

'Yan sandan jihar Kano sun ce sun shiga neman wani mutum mai suna Malam Lawan Sheka, bisa zargin turke ɗansa tsawon shekara 15 cikin yanayin da bai dace da ɗan'adam ba.

Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni kwamishinan 'yan sandan Kano ya ba da umarnin mayar da maganar hannun babban sashen binciken laifuka na Bompai don faɗaɗa aikinsu.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi zargin cewa mahaifin Ibrahim Lawan ya tsare shi ne da niyyar yi masa kisan mummuƙe.

"To bincikenmu ya nuna mana cewa ya kulle shi ne da niyyar ya kashe shi. Saboda ya bar shi ba abinci, ba komai. Kuma gidanma ba ma na mahaifinsa ba ne, na ita mahaifiyar matashin ne da ta rasu," in ji shi.

Ya ce har yanzu suna tsare da Binta Sulaiman, matar Malam Lawan Sheka wadda "bayan auro ta (ne) suka ajiye shi cikin wannan yanayi".

Baya ga matar, 'yan sanda sun ce suna kuma yi wa mai unguwar Sheka ta Kudu Malam Bello Da'u da wasu mazauna unguwar tambayoyi kan wannan lamari.

Tun ran Lahadi ne 'yan sanda suka yi awon gaba da mai ɗakin mahaifin Ibrahim Lawal, don yi mata tambayoyi, sai dai wata sanarwa da DSP Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana matar a matsayin ɗaya daga cikin wadda ake zargi..

Wani maƙwabcin gidansu matashin da ke unguwar Shekar Ɗan Fulani a Kumbotso ya faɗa wa BBC cewa duk wani yunƙuri da mahaifiyar Ibrahim Lawal ta yi a baya don kuɓutar da ɗanta, abin ya ci tura.

Ya ce yayin kuɓutar da matashin, 'yan sanda sun same shi a ɗaki cikin mummunan yanayi, kuma ana zuba masa abinci cikin wani babban kwano tamkar dabba. "Ko tafiya ba ya iya yi".

Matashin dai shi ne na biyu cikin kwana biyu da 'yan sanda suka kuɓutar a irin wannan yanayi na turkewa a gida cikin yanayin da bai dace da ɗan'adam ba.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda aka fitar da mutumin daga ɗaki yana nishi jikinsa a ƙanjame.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Abdullahi Kiyawa ya ce sun ceto matashin ne a Sheka Unguwar Fulani da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso bayan sun samu bayanai daga jama'ar gari.

Ya ce suna ci gaba da bincike amma da zarar sun kammala za su gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu gaban kotu.

Mai unguwar yankin, Malam Bello Da'u Sheka ya ce suna da masaniyar cewa matashin kamar mahaifinsa, mahaddacin Ƙur'ani ne, kuma akwai raɗe-raɗin cewa Ibrahim yana da taɓin hankali.

Ya ce a baya abokan Ibrahim Lawal sun taɓa yunƙurin tara gudunmawa don kai shi asibiti, amma mahaifinsa ya ce yana nema masa magani.

Basaraken ya ce ya shafe kimanin shekara takwas zuwa tara, bai sa idonsa a kan matashin ba. "Ni da na ga ba na ganinsa, abin da na ɗauka ko ubansa ya kai shi makaranta ta allo".

Mai magana da yawun 'yan sandan Kano ya ƙara da cewa tuni suka kai mutumin asibiti sannan kuma sun fara bincike game da lamarin.

'Yan sanda dai ba su samu mahaifin Ibrahim Lawal a gida ba lokacin da suka je kuɓutar da matashin ranar Lahadi.

Wannan na zuwa ne kwana uku kacal bayan ceto Ahmad Aminu - wani mutumin da iyayensa suka tsare shi tsawon shekara uku.