Jubril Aliyu Kebbi: Me ya sa ake zaman doya da manja tsakanin kishiyoyi da 'ya'yan mijinsu?

Jibril Aliyu yaron da kishiyoyin mahaifiyarsa suka ci zarafinsa na murmurewa

Asalin hoton, KBSTGOVT

Bayanan hoto, Jibril Aliyu yaron da kishiyoyin mahaifiyarsa suka ci zarafinsa na murmurewa
    • Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Hausawa na da kirari daban-daban da ke nuna irin alakar da ke tsakanin ɗan kishiya da kuma matar miji.

Irin wadannan kirari sun hada da ɗan kishiya rikon mai hakuri, da kuma kishiyar uwa ba uwa ba ce.

Watakila wadannan kirari suna cikin abubuwan da suka dasa kiyayya tsakanin bangarorin biyu, inda a lokuta da dama ba sa ganin amfanin juna.

Hakan ya sa cin zarafin ɗa ko 'yar miji da kuma raina matar uba suka kasance wasu abubuwa da suka yi fice a yankunan da dama a Najeriya da ma Afirka, ciki har da kasar Hausa.

Bincike ya nuna cewa mata da dama na kishi da 'ya'yan mijinsu don haka suna ɗaura musu tsana da ƙiyayya da cin zarafi. Watakila hakan ba ya rasa nasaba da irin zaman da suka yi da mahaifiyarsu.

A gefe guda, 'ya'yan miji da dama ba sa ganin kishiyar mahaifiyarsu da gashi.

Babu wani ƙiyasi ko adadin irin wannan cin zarafi da ake samu a gidaje a Najeriya, amma galibi abu ne da ba sabo ba kuma ana yawan magana a kai.

Sai dai sake bijiro da batun a wannan lokaci ya zo ne bayan 'rashin imanin riƙon sakainar kashin da aka yi wa wani yaro', ɗan kimanin shekara goma mai suna Jibril Aliyu.

An bandako wannan labarin ne a jihar Kebbi bayan gano wasu kishiyoyi biyu sun ɗaure dan mijinsu a turken awaki tsawon shekara biyu, kafin kuɓutar da shi a ranar Lahadi.

Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an hukumar kare haƙƙin ɗan'adam suka kuɓutar da Jibril sanye da wata jar riga yana tafiya da ƙyar saboda sirancewa.

Wannan hali da aka tsinci Jibril ya tayar da hankali inda mutane ke ta mayar da martani da alla-wadai da mummunan hali da kishiyoyin mahaifiyar Jibril suka jefa shi a ciki.

Haka kuma gwamnatin jihar ta Kebbi ta kaddamar da bincike kan lamarin.

To ko a ina matsalar take?

line

Zaman kishi da 'ya'yan miji

Hada miji guda na haddasa ƙiyayya da gaba tsakanin mata
Bayanan hoto, Hada miji guda na haddasa ƙiyayya da gaba tsakanin wasu matan

Cin zarafin 'ya'yan miji kusan ya yi fice a kasar hausa, da ma wasu yankunan Afirka inda mata suka daurawa kansu ko zuciya tsananin kishi, wasu lokutan ma rigimar a kan gado ake yin ta.

Bilkisu Salisu Funtua wata fitacciyar marubuciyar litattafan Hausa a arewacin Najeriya, ta ce al'amarin akwai rikitarwa domin yara na shiga cikin bakar azaba saboda dalilai na son rai.

''Nakan yi tunanin ina makwabta ina batun 'yan unguwa domin abin akwai ɗaure kai sosai.''

Bilkisu Funtua ta ce halin da wasu kishiyoyi ke jefa ɗan mijinsu ya wuce sharrin almajiranci domin za ka iske uban ma an mallake shi ba ya iya tabuka komai ko cewa uffan.

''Uba ya tara mata marasa imani kowa wanda ya haifa ya sani don haka ayi ta cin zalin juna, Idan ka yi magana a ce yaro ya gaggara don kawai an ga mahaifiyarsa ba ta gidan.''

Bilkisu ta ce akwai jahilci da kuma yadda duniya ta koma daga kauri sai gwiwa kowa nasa ya sani ko tsakanin 'yan uwa ciki daya babu soyayya sai ƙiyayya.

Sai dai kuma wasu na ganin su ma yaran ba sa girmama matan mazajensu, abin da ke sa wa zuciya ta debe su su aikata mummunan aiki a kansu.

line

Jahilci

Ana danganta tsananin kishi da karuwar jahilci musamman a yankunan da ake auren mace sama da guda.

Masu nazari na cewa idan ka tara mace 10 da kyar za ka samu 3 na kirki wanda ke zama zuciya guda da ɗan miji ko 'yar miji ba ga birni ko kauye ba.

Mata sun ɗaurawa kansu mugun kishi, akwai rashin ilimin addini da tsoron Allah, hatta shi kansa miji da abokiyar zama ha'intar juna ake yi, in ji Bilkisu.

Abin mamaki shi ne ina 'yan uwa suke lokutan da ake samun irin wannan cin zarafi a kan yara.

line

Zamani

A ko da yaushe ana samun ci gaba rayuwa amma batun kishi na sake taɓarɓarewa.

A zamanin baya akwai yaran da suka taso ba sa iya bambance mahaifiyarsu saboda irin zaman amana da ake yi.

Amma Rahama Abdulmajid da ke fafutikar kare haƙƙin mata ta ce da ma kishiyoyi kusan maƙiyan juna ne don haka babu batun soyayyar gaskiya tsakaninsu.

Sai dai ta ce cutar da bil adama musamman yara akwai rashin tarbiya da imani ko matsalar ƙwaƙwalwa tattare da wacce ta aikata hakan.

Rahama ta ce tarbiya ta lalace, mata zamani ba sa kaunar abokiyar zama su burinsu daga su sai miji ko 'yan uwansa ba sa kauna, balanta a ce yana da yara.

Bilkisu Funtua ma da irin wannan ra'ayi domin ta shaida cewa wasu matan daga lokacin da suka sanar da kawaye za su yi aure abin da ake soma tambaya shi ne akwai ''ulcer da hawan jini wato ma'ana iyayensa kenan''.

line

Kiyayya

Yara na shiga akuba a hannu wasu matan ubansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara na shiga akuba a hannu wasu matan ubansu

Hada miji guda na haddasa ƙiyayya da gaba tsakanin mata amma kuma wasu kan ce ya danganta da yanayin miji da kuma yadda ya shimfida dokoki a gidansa.

Rahama ta ce idan aka samu namiji da ba shi da karfi faɗa a ji ko iya tafiyar da gidansa a galibin lokuta ba a samun zaman lafiya.

Sannan akwai mijin da ke fifita wani cikin 'yaransa, hakan ma a cewar Rahama na janyo ƙiyayya da tunzura zuciya ta yi ramuwa.

Mata kuma ba su fiya la'akari da cewa wannan ɗan mijinsu ne, abin da suke mayar da hankali shi ne wannan yaron ko yarinya 'yar kishiya ce.

Munin bakin kishi ba wai da ɗan miji kawai ake yi ba, har 'yan uwa da iyayyensa ƙyamartar su ake yi, in ji Bilkisu Funtua.

line

Mafita

Bilkisu Funtua ta ce daidaita kishi ko samar da mafita abu ne mai wahala.

Masu imanin kadan ne duba da irin fitintunun da ake samu a gidan ma'aurata, cutar da miji ko miji ya cutar da mata ba bakon abu bane.

Akwai bukatar faɗakarwa nasihohi da sake ilimantarwa ko da ba zasu dauka ba.

Sannan ita ma gwamnati ana ganin akwai bukatar ta sa ido ta bijiro da hanyoyi taƙaita irin wadanan mugayen halaye da ke cutar da yara.

line

Sharhi

Kishi ya zauna a zukatan mata da dama da ke ganin cewa kishi shi ne mafita a garesu, don haka babu zance imani ko tsoron Allah, musamma a arewacin Najeriya.

Abin mamaki shi ne yadda zaka iske wasu iyaye na goyon-bayan 'ya'yansu ko rashi ƙwaba ko ganar da 'ya mace cewa kishiya da maƙiya ba ce.

Zargin cuzgunawa 'ya'yan kishiyoyi dai ba bakon abu ba ne a arewacin Najeriya.

A galibin lokuta baƙin kishi kan ƙare ne akan yaran da basu ji ba basu gani ba misali halin da Jibril ya tsinci kansa saboda ƙiyayyar kishiyoyin mahaifiyarsa.

Labarin Jibril akwai sosa rai domin kusan abin da ake magana kenan yanzu haka a shafukan sada zumunta a Najeriya.

Tuni aka ƙirƙiri wani maudu'i mai taken #JusticeforJibril inda mutane ke neman a bi masa haƙƙinsa da sauran irin wadanan yara da ke shiga irin wannan aƙuba saboda tsananin kishi.

Marubuciya Bilkisu Funtua ta ce akwai bukatar faɗakarwa da ilimantarwa tun daga iyaye kafin aurar da yarinya. Sannan akwai bukatar sa ido kan yanayin zamanta kewa a gidaje.

line

Karin labaran da zaku so karantawa