Fashewar sinadarai a Beirut: Amaryar da ta yi ido biyu da mutuwa

Bayanan bidiyo, Amaryar da ta yi ido biyu da mutuwa

Israa Seblani tana tsaka da daukar hotunan bikinta ranar Talata lokacin sinadarai suka yi bindiga a Beirut, babban birnin Lebanon.

Ta shaida wa BBC cewa ta ji kamar za ta mutu.