Darajar Naira: Yadda 'yan Najeriya ke tsokaci kan farfaɗowar da kuɗinsu ke yi daga shaƙewar da dala ta yi masa

Kuɗaɗen ƙasar waje

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Naira ta ƙara daraja da kusan 47
Lokacin karatu: Minti 3

Tun ranar Litinin ne takardar kuɗi ta Naira a Najeriya ta ƙara daraja kan kuɗaɗen ƙasashen waje yayin da ake canzar da ita a kan N430 kan kowacce dala ɗaya a kasuwar bayan fage da ke Abuja da wasu sassan kasar.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar ne cewa zai ci gaba da sayarda kuɗaɗen waje ga 'yan kasuwar canji kuɗaɗen da ke da rijista.

Su ma kuɗaɗen Fan na Ingila da Yuro na ƙasashen Turai ana canzar da su kan N535 da kuma N520 kan kowanne ɗaya.

Ranar Talata, an canzar da dala ɗaya a kan naira 432 a kasuwar Wapa ta jihar Kano, yayin da a Legas aka canzar da ita kan naira 440.

Kazalika ana canzar da dalar kan naira 430 a Abuja ranar Laraba.

Sai dai wannan na faruwa ne a kasuwannin bayan fage, yayin da farashin dala na gwamnati yake kan N380 kan kowacce dala ɗaya.

A cewar wasu bayanai da shafin Abokifx mai bin diddigin harkar canji ya fitar, Naira ta ƙara daraja da 12 idan aka kwatanta da N477 kan dala ɗaya da aka canjar da ita ranar Juma'a, 28 ga Agusta.

Kuka da murna

Wannan ta sa 'yan kasuwa da suka sayi dalar ke fargabar faɗuwa idan har darajar Naira ta ci gaba da hawa, yayin da wasu kuma ke murnar dawowar kimarta.

Aminu Gwadabe, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar canji a Najeriya mai suna Association of Bureau de Change Operators of Nigeria, ya faɗa wa kafar Bloombarg cewa 'yan kasuwar ba sa son sayen kuɗaɗen ƙasar waje a yanzu saboda rashi tabbas.

"Da yawa daga cikin 'yan kasuwar da ke da kuɗaɗen ƙasar wajen suna ta fito da su kasuwa saboda ba su san yadda farashin zai kasance ba, su kuma mutane ba sa son saya," in ji shi.

Su ma masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya musamman Twitter sun yi ta tsokaci kan batun yadda har sai da "Naira" ta kasance cikin manyan maudu'an da aka fi tattaunawa a kansu a shafin na Twitter.

Wannan cewa yake: "Mun fi buƙatar tabbataccen farashin Naira ba lallai sai mai matuƙar daraja ba."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kasancewar faɗuwar kuɗaɗen ƙasashen waje ba mazauna Najeriya kaɗai ta shafa ba, kuɗaɗen da iyaye ke biya wa yaransu na karatu a ƙasashen waje ma zai ragu idan Naira ta ci gaba da yin daraja.

Wani fitaccen mai amfani da shafukan zumunta Dr. Dípò Awójídé ya shawarci ɗaliban da su mayar da hankali kan karatunsu saboda duk da haka Fan na Ingila yana da daraja sosai.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Tasirin ƙaruwar darajar Naira

Masanin tattalin arziki Dr. Shamsuddin Muhammad na Jami'ar Bayero ta Kano ya shaida wa BBC cewa faɗuwar darajar dala za ta yi amfani ga talakawa da kuma gwamnatin Najeriya.

Malamin jami'ar ya ce idan farashin kayayyakin ƙasar waje ya sauka ko ya hau sai ya shafi mutane da kuma abubuwan da suke sarrafawa a cikin gida.

"Duk sanda kaya suka yi sauƙi to an fi samun riba saboda mutane sun fi saya," in ji shi.

Kazalika ya ce akwai yiwuwar Nairar ta gaza riƙe darajar tata matuƙar CBN ya dakatar da bayar da kuɗaɗen waje ga 'yan kasuwar "abin da ba a fata," a cewarsa.

"Da ma ai shi kuɗi matsoraci ne kamar yadda muke faɗa a ilimin tattalin arziki. Tsoro ne yake kawo faɗuwar farashin, tun da CBN ya ce zai bayar da dalar shi ne mutane suke fitowa da ita don gudun kada su yi asara."