Muhammadu Buhari: Saƙon wasu 'yan Najeriya zuwa ga Shugaban ƙasarsu

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yana neman wa'adi na biyu
Lokacin karatu: Minti 3

Dubban masu bibiyar shafukan sada zumunta na BBC Hausa sun bayyana korafe-korafensu kan mawuyacin halin da suke ciki sakamakon tsadar rayuwa.

Hakan na faruwa ne a yayin da suke tofa albarkacin bakinsu bayan mun bukaci 'yan Najeriya su bayyana mana sakonsu ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da a ce za su samu damar ganawa da shi.

Mun yi wa wannan maudu'i take da 'Wasika Zuwa Ga Shugaban Kasa' wanda muka wallafa a shafukanmu na Facebook da Twitter da kuma Instagram.

Dubban masu bibiyarmu a shafukan sada zumunta ne suka bayyana ra'ayoyinsu iri daban-daban.

A shafinmu na Facebook kadai, mutum fiye da dubu bakwai ne suka yi tsokaci kan sakon da za su gaya wa Shugaba Buhari idan suka samu damar ganawa da shi.

Galibin mutanen da suka tofa albarkacin bakinsu sun nuna matukar bacin ransu kan rashin tsaro da karin da aka yi na farashin wutar lantarki da man fetur da kayan masarufi, musamman wadanda aka sanar da karinsu a makon jiya.

Wani mai bibiyarmu, Aminu A Yusuf Kwashabawa, ya fara da cewa idan ya samu ganawa da Shugaba Buhari zai ce masa: "Ya ji tsoron Allah, ya karfafa tsaro ya bude iyakokin kasar nan. Wallahi talakawa na cikin musiba."

Shi ma Suleiman Musa ya ce: "Baba[Buhari] a gaskiya talakawa na cikin mawuyacin hali na rashin tsaro, tsadar abinci ta kai wani halin da sai dai muce Lahaula Wala kuwata illa billah. Don Allah a taimaka a bude boda domin samun saukin kayan abinci."

Buhari
Bayanan hoto, Rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki na kan gaba a game da abubuwan da mutane ke korafi a kansu

Sai dai wasu sun yaba wa shugaban kasar bisa ayyukan da suka ce yana yi na gyaran Najeriya, inda Malam Adamu Dumbulun ya ce idan ya samu ganawa da shugasban kasar, "zan fada masa Baba mu talakawa, muna jin dadin mulkinka sannan mun kara gano manufofinka ta gyaran kasar nan ne domin babu wani jin dadi da yake zuwa a saukake."

A shafinmu na Twitter, @AiyushaAisha ta ce: "Wasika zuwa ga shugaban kasa. A gaskiya Baba tashin farashin kayan masarufi da na lantarki, yana jijjiga mazan har da mata. Yau ga shi saurayina ya daina zuwa zance wai saboda farashin mai ya karu. Baba wai so kake mu tsufa a gidan iyayenmu ne ba mu yi aure ba?"

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Ita ma Binta Abdulkadir ta bayyana cewa idan ta hadu da shugaban kasa za ta gaya masa cewa "matasa ba aikin yi ga tsadar rayuwa".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan layi ne

Ƙarin haske

A makon jiya fadar shugaban Najeriya ta yi karin haske kan abin da take ganin ya jawo yanayin tsadar rayuwa da tashin farashi da 'yan kasar ke ta korafi a kai.

A wata hirarsa da BBC Hausa, mai bai wa shugaban kasar shawara kan harokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce abu uku ne suka jawo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta, amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.

Malam Garba Shehu ya zayyana wa BBC dalilai uku da suka sa 'yan Najeriya suka samu kansu a hali na tsadar rayuwa kamar haka:

1. Batun taki: Karayar tattalin arziki da annobar cutar korona ta jawo wa kasashe na nesa da kusa ya shafi shigo da ma'adinai da ake amfani da su wajen sarrafa taki.

Hakan ya sa taki ya yi tsada a noman rani har zuwa yanzu, ta yadda wadansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka mata dole ta sa suka saida wa makiyaya shinkafar. An yi haka a kasar nan.

2. Mugunta tsakanin mutane: Akwai 'yan kasashen waje da ake gani suna yi. Sayen abinci ake yi ana boye shi a kasar nan.

Kuma gwamnati na nan na daukar mataki kan wannan.

3. Kafa masana'antun shinkafa: An samu ci gaba wajen kafa masana'antun sarrafa shinkafa da yawa a kasar nan. Kamar a Kano akwai wajen 18 wanda kowanne a ciki yana sarrafa shinkafa daga tan 180 zuwa 400 a kowace rana. Suna daukar ma'aikaci bai gaza 200 ba.

Amma yanzu kowa so yake ya ga cewa masana'antarsa ba ta tsaya ba. Kasuwa ake shiga suna zuba kudi ko nawa ne ba ruwansu don su ci gaba da sarrafa masana'antunsu biya suke a ba su shinkafa danya.

Wannan layi ne