Bah Ndaw: An naɗa sabon shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya a Mali

Asalin hoton, AFP
An naɗa shugaban riƙon ƙwarya a Mali, wanda shi zai jagoranci shirya zaɓe da miƙa mulki ga duk wanda al'ummar ƙasar suka zaɓa.
Tawagar da aka ɗora wa nauyin naɗa shugaban da zai jagoramci Mali cikin watanni masu zuwa tun bayan juyin mulkin da aka yi, sun gana a ranar Litinin inda suka naɗa shugaban ƙasar farar hula na riƙon ƙwarya da mataimakinsa.
Tsohon ministan tsaro Bah Ndaw aka naɗa a matsayin sabon shugaban na riƙon ƙwarya a Mali da kuma Kanal Assimi Goita a matsayin mataimakinsa.
Sai dai dukkaninsu tsoffin sojoji ne da suka riƙe manyan muƙaman soja a Mali.
An yi wannan naɗi ne bayan da sojojin juyin mulki suka fuskanci matsin lamba daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika Ta Yamma Ecowas.
Ecowas ta matsa ƙaimi cewa dole ne ya kasance farar hula ne za su jagoranci gwamnatin rikon ƙwarya da za ta jagoranci sabon zaɓen shugaban kasa.
Sauran muƙaman da aka naɗa sun haɗa Firaminsita inda Ecowas ta sake dagewa cewa sai farar hula za a bai wa.
Ƙungiyar Ecowas ta ce za ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙabawa Mali da zarar sojoji sun mika mulki ga farar hula.
Sai dai abin tambaya, shi ne ko sabon shugaban da aka nada na riƙo tsohon soja za a yi masa kallon farar hula?
Ana sa ran mai shiga tsakani kan rikicin Mali na ƙungiyar Ecowas, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a cikin wannan makon zai tafi ƙasar.











