Rikicin Mali: An kashe sojoji goma a ƙasar

..

Asalin hoton, Getty Images

Akalla sojoji goma aka kashe a Mali yayin wani hari da wasu masu iƙirarin jihadi suka kai a ƙasar.

Rundunar sojin Mali ta bayyana cewa harin ya faru ne kusa da wani gari da ake kira Guire wanda ke kusa da iyakar ƙasar da Mauritania.

Wannan shi ne hari ma fi muni da aka kai tun bayan da sojojin ƙasar suka yi juyin mulki ga Tsohon Shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita.

Tuni dama dai 'yan ƙasar na ta nuna ɓacin ransu dangane da yadda gwamnatin ƙasar ke tunkarar yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Ina batun hamɓararen shugaban Mali?

An sallami Tsohon Shugaban Mali da aka hamɓarar Ibrahim Boubacar Keita daga asibiti, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

An kai Mista Keita asibiti ne domin duba lafiyarsa sakamakon barazanar da yake samu ta shanyewar rabin jiki, a halin yanzu dai, ya tafi Haɗaɗdiyar Daular Larabawa domin a ci gaba da duba lafiyarsa.

Shugaban mulkin soja na Mali Kanal Assimi Goita, ya ziyarce shi a ranar Alhamis inda ya yi masa fatan samun lafiya.

Sojoji ne suka kama Mista Keita a ranar 18 ga watan Agusta kafin daga baya ya bayyana cewa ya yi murabus daga shugabancin ƙasar.