Mali: Abubuwan da suka kamata ku sani game da rikicin siyasar kasar

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Kasashen duniya na sake nuna damuwar su kan hanyoyin kawo karshen rikicin siyasar Mali, wanda ake ganin na neman sake bude kofa ga kungiyoyin ta'addanci, bayan narka dumbin kudaden da Faransa - wacce ta mulki kasar - ta yi domin tabbatar da tsaro a kasar.
Yanzu haka dai shugabannin kasashen yammacin Afirka biyar sun isa kasar da nufin ganin ko za su yi wa rikicin tufka, ganin cewa a rikicin Mali idan aka ci gaba da tafiya a haka to zai shafi sauran kasashen makwabta.
Adawar da Shugaba Keita ke fuskanta na sake ta'azzara, tun farkon wannan watan ake tafka rikici, abin da ya kai ga mutuwar masu zanga-zanga 12 a wata arangama da jami'an tsaro.
Kokarin da aka yi a baya na shiga tsakani domin sulhunta bangarorin da ke tayar da jijiyoyin wuya ya ci tura, yayin da 'yan adawa suka dage kai da fata sai Shugaba Keita ya yi murabus.
Dalilan da suka bayar na neman shugaban ya bar mulki, sun hada da matsalolin tsaro da ke ta'azzara da cin hanci da rashawa da kuma zaben 'yan majalisa a watan Maris da ya haifar da rigima.
Masu sharhi dai sun nuna fargaba domin a cewarsu muddin ba a dage wajen warware wannan matsala ta siyasar Mali ba, to za ta kasance wata dama ga kungiyoyi masu dauke da makami wajen ruguza kasar da kuma ingiza rashin tsaro a yammacin Afirka.
Masana siyasar Afirka kamar Dokta Abubakar Kari ya shaida wa BBC cewa, rikici kusan gwagwarmaya ce tsakanin bangarori daban-daban kan shugabanci.
Dokta Kari ya ce idan aka yi waiwaye kan tarihin Mali kamar shekaru 20 da suka gabata dama ana samun irin wadannan rigingimu.

Me ya sa aka damu?

Asalin hoton, Reuters
Rikici ko neman sulhu a kasar Mali a yanzu zai kasance ne da Mahmoud Dicko, mutumin da ke jagorantar boren kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, in ji Dokta Kari.
Mahmoud Dicko dai bai taba rike wani ofishin gwamnati ba amma yana da karfin fada a ji a kasar.
Sannan wasu abubuwan da ya sa rikicin ya yi kamari akwai kungiyoyin 'yan tawaye da 'yan ta'adda a kasar da ke muggan ayyukan.
Rashin zaman lafiya kasar ya shafi kusan duk yammacin Afirka wannan dalili ne ya sa duniya ta tyar ada hankalinta.
Shugabannin Afirka na nuna damuwarsu ne saboda Mali tana da girman kasa da iyaka mai nisa, duk wani abin da ya shafeta sai ya shiga makwabta, in ji Kari.
Dokta kari ya ce 'A Najeriya ma ana rade-radin cewa ana shigar da makami kasar daga Mali.'

Kokarin Sulhu ko Mafita

Asalin hoton, Reuters
A 'yan shekarun nan kungiyar hadin-kan kasashen Afirka da ta Afirka ta yamma na sa ido kan zabe na gari da nuna kiyayya, da nuna rashin gamsuwa da matakan wasu shugabannin.
Wannan dalili ne ya sa da farko wata tawagar Ecowas karkashin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ta kai ziyara kasar, kuma ta yi watsi da bukatar cire Keita daga Mulki.
Sai dai tawagar ta shawarci kafa gwamnatin hadaka - bukatar da 'yan adawa suka yi watsi da ita.
Dokta Kari ya ce, yanzu haka akwai zargin da ake cewa shugabannin Afirka na goyon-bayan gwamnatin Boubacar Keita.
"In dai haka ne kuma sabuwar tawagar da aka tura ta je da wannan batu, to zaman lafiya zai gagara, amma idan suka fahimci matsalar kamar cire Keita ce alheri to ya zama dole su bi inda sun shirya kawo karshen rikicin."

Karin haske
Yanzu haka yammacin Afirka na cikin barazana saboda kungiyoyin 'yan bindigar Mali wadanda yawancinsu ake zargin na da alaka da IS da Al-Qaeda, sannan ga zargin fataucin makami ta kasar.
Masana dai na ganin idan kasar ba lafiya ba wanda zai samu sukuni.
Masu zanga-zangar gamayya ce da ta fito daga bangarorin addinai daban-daban, siyasa da kungiyoyin farar hula.
Kuma ana yi wa jagoran zanga-zangar, wato Dicko, kallon wanda ke jan ragamar nuna turjiya, wanda masu adawa da gwamnati ke ganin hakan ita ce mafita a gare su.

Asalin hoton, Reuters
Dicko da ake sa ran - ya tattauna da shugabannin Najeriya da Ivory Coast da Senegal da Ghana da Nijar - har yanzu a bayyane bai nuna alamun akwai wasu sharudan da za su iya sauya ra'ayinsa ba.
Ya kuma sha watsi da zargin da ake masa na ko yana neman mukamin siyasa ne.
Tawagar wannan lokaci karkashin shugaban Nijar, Muhammadou Issouffou, wanda shi ne shugaban Ecowas, za ta tattauna da bangarorin da wannan rikici ya shafa domin ganin an cimma mafita.
Sauran shuggabannin da ke cikin tawagar sun hada da na Najeriya da Senegal da Ghana da Ivory Coast.












