Goodluck Jonathan: An naɗa tsohon shugaban Najeriya domin sasanta rikicin Mali

Jonathan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duniya ta yaba wa Jonathan saboda amincewa da shan kaye a zaben 2015

An nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin wakili na musamman da zai sasanta rikicin siyasar kasar Mali.

Ana sa ran zai tattauna da manyan masu ruwa da tsaki a kasar cikinsu har da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta, shugabannin jam'iyyun hamayya, kungiyoyin fararen hula da kuma malaman addini domin shawo kan rikicin.

Mali tafada cikin rikicin siyasa a makonnin baya bayan nan inda masu zanga-zanga suke kira ga Shugaba Keïta ya sauka daga mulki kan batutuwa da dama ciki har da zaben da ake ce-ce-ku-ce a kansa.

Masu zanga-zangar sun samu kwarin gwiwa ne musamman saboda gazawar gwamnati wajen shawo kan rikicin kabilanci da na addini da ke addabar kasar.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, Jean-Claude Kassi Brou ne ya sanar da nadin Mr Jonathan.

"Ina amfani da wannan dama, bayan tuntubar shugaban kungiyar nan mai girma Issoufou Mahamadou, shugaban Jamhuriyar Nijar, matsayin da muka dauka na nada ka a matsayin wakili na musamman don magance rikicin Mali," a cewar wasikar da aka wallafa a jaridun kasar.

Mr Jonathan ya samu yabo daga kasashen duniya a shekarar 2015 bayan ya amince da shan kaye a zaben da Janar Muhammadu Buhari ya lashe.