Karfin soji ba zai samar da zaman lafiya ba — Jonathan

Asalin hoton, Independent Newspaper
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce tarin makaman nukiliya da bindigogi ba shi ne zai samar da zaman lafiya a duniya ba.
Mr Jonathan, wanda ya bayyana haka ranar Litinin a wurin wani taron kasashen duniya mai taken World Summit 2020 a birnin Seoul na Koriya ta Kudu, ya kara da cewa zaman lafiyar duniya "yana samuwa ne a cikin zukatanmu."
Ya ce "Ya kamata mu binciki zukatanmu sannan ko da yaushe mu nuna so da kauna domin kare mutanenmu."
Mr Jonathan, ya kuma bayyana jin dadi da godiyarsa dangane da damar halartar taron da aka ba shi, inda ya ce ya yi murna sosai da aka ba shi dama ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajen halartar taron na zaman lafiya.
Jonathan ya bayyana halartar taron da ya yi din ne a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2
Tsohon shugaban na Najeriya, ya sha yabo sosai lokacin da ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa na 2015, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.
Tun bayan amsar mulki daga hannun Goodluck Jonathan, ba a taba jin wata mummunar kalma ta fito daga bakin Shugaba Buhari kan Jonathan din ba duk da cewa gwamnatin Buhari ta sha nuna wa tsohuwar gwamnatin yatsa kan wasu tuhume-tuhume.
Sai dai a wasu lokutan baya, Shugaba Jonathan ya sha yin hannunka mai sanda ga gwamnatin Buhari duk da cewa shi ma bai taba kama suna ba.