Ecowas 'ba za ta goyi bayan tsige shugaban Mali ba - Jonathan

Boubacer Keita

Asalin hoton, Reuters

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda a baya-bayan nan ya jagoranci wata tawagar sasanta rikicin siyasa a Mali, ya ce Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirika Ta Yamma (ECOWAS) ba za ta goyi bayan tsige Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ba.

Ƙungiyoyin hamayya sun sha yin kira ga Shugaba Keita da ya sauka daga mulki saboda yadda ya kasa magance rikice-rikicen da aka dade ana fuskanta a Mali, wadanda masu tayar da kayar baya ke assasawa da kuma wanda zabe ya jawo.

Amma Mista Jonathan ya ce dole a zabi shugabanni kuma a sauke su ta hanyar bin tsarin mulki, idan ba haka ba kuma za a samu rashin doka da oda a kasashe.

Ya kara da cewa Ecowas ba za ta yanke hukunci kan tsige wani zababben shugaba ba, inda ya ci gaba da cewa ko Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya ba za su iya yin haka ba.

Short presentational grey line

Me 'yan adawar ke so?

Gamayyar kungiyoyin hamayya sun yi watsi da shawarwarin da tawagar Ecowas ta gabatar musu na samar da gwamnatin hadin gwiwa da sake fasalin Kotun Kolin kasar wadda ta sauya sakamakon zaben majalisar dokoki da aka yi a watan Maris.

Sun ce bukatarsu mai sauki ce - dole Shugaba Boubacar Keita ya yi murabus - inda suke bayar da hujja karuwar rashin tsaro da cin hanci da kuma magudin zabe.

Zanga-zanga a Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi ta zanga-zanga a Mali a makonnin da suka gabata inda ake kira ga Shugaba Keita da ya yi murabus

A yanzu dai bangaren hamayya na Mali sun ce za su dakatar da zanga-zanga, a wata yarjejeniya gabanin bikin Babbar Sallah.

Ana sa ran tawaga ta biyu da ta hada da shugabannin kasashen Afirka Ta Yamma da suka hada da na Nijar da Senegal da Ghana da Ivory Coast za su isa Mali a ranar Alhamis, a wani kokarin na sasanta rikicin siyasar.

Short presentational grey line

Jonathan ya gabatar wa Buhari rahoto

A ranar Litinin ne tsohon Shugaban Najeriyar ya kai wa Shugaba Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja, inda suka tattauna a wata ganawar sirri.

Saƙon Twitter da Buhari ya wallafa ya nuna cewa Jonathan ya je Fadar Aso Rock Villa domin miƙa rahoton aikin sasanta rikicin siyasa ne wanda ƙungiyar ECOWAS ta tura shi ƙasar Mali a makon da ya gabata ga Buhari.

"Na karɓi rahoton wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, game da rikicin siyasar Mali kuma za mu nemi shugaban ƙungiyar, Shugaban Nijar, ya yi mana cikakken bayani a matsayinsa na shugaba," in ji Buhari.

Wannan layi ne