Masu zanga-zanga sun tilasta wa talbijin ɗin Mali katsewa

Opposition supporters protest in Mali

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Magoya bayan 'yan adawa sun kuma yi ƙoƙarin kutsa wa cikin ginin majalisar dokoki

Masu zanga-zanga a Mali sun tilasta wa kafar yaɗa labaran ƙasar katse shirye-shiryenta yayin wani gagarumin jerin gwano a Bamako, babban birnin ƙasar.

'Yan sanda sun hahharba bindiga kuma sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga -wasunsu ma na ƙoƙarin kutsawa cikin ginin majalisar dokokin ƙasar.

Wannan ne maci na uku a cikin wata guda don neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya sauka daga kan mulki.

Akwai rashin gamsuwa kan yadda ake tunkarar rikicin masu iƙirarin jihadi da ya shafe tsawon lokaci, da matsalolin tattalin arziƙi da kuma taƙaddama game da zaɓukan 'yan majalisa.

Wani sabon ƙawancen 'yan adawa ƙarƙashin jagorancin wani malami mai ra'ayin 'yan mazan jiya, Mahmoud Dicko, a wannan mako ya ce ya janye buƙatarsa ta neman Shugaba Keita ya sauka daga mulki.

Sai dai har yanzu ta dage cewa sai an wanzar da ƙarin sauye-sauye bayan ta yi watsi da sassaucin da shugaban Mali ya yi ciki har da batun kafa wata gwamnatin haɗaka.

Mene ne sabon abu da ke faruwa a Mali?

Dubban masu zanga-zanga ne suka fantsama kan titunan Bamako, kamar yadda editan BBC na Afirka, Will Ross ya ruwaito.

Wasu daga cikinsu na wani ɗan lokaci har sun kai ga ginin kafar yaɗa labaran ƙasar, ORTM, lamarin da ya tilasta mata katse shirye-shirye a lokacin. An rufe tituna da shingayen da ke ci da wuta.

Protests on the streets of Bamako

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan shi ne maci na uku a tsawon wata ɗaya, inda mutane suke kira ga Shugaba Keita ya sauka daga mulki

Haka kuma an samu wasoson dukiya, har ma da rahotannin matasa na ƙoƙarin kutsa kai cikin ginin majalisar dokoki.

Majiyoyi guda biyu sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kashe a ƙalla mutum ɗaya a wajen ginin majalisa.

Me ya sa mutane ke zanga-zanga?

Wannan zanga-zanga ita ce ta uku tun cikin watan Yuni.

Zanga-zanga ta fara ne bayan ƙawancen 'yan adawa sun yi watsi da sassaucin da Shugaba Keita ya ɓullo da shi don kawo ƙarshen rikita-rikitar siyasa kan dambarwar zaɓen 'yan majalisar dokoki a watan Maris.

A makon nan 'yan adawa sun ce tafiyarsu ta jingine buƙatarta ta neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya sauka. Sai dai har yanzu ta buƙaci gudanar da zanga-zanga saboda tana neman ƙarin sauye-sauye.

Keita ya hau mulki wa'adi na biyu tsawon shekara biyar ne a 2018 sai dai yana fuskantar ƙarin adawa game da bazuwar tarzomar masu iƙirarin jihadi da kuma matsalar tattalin arziƙi.

Al'ummar Mali dai na fatan cewa masu iƙirarin jihadi, waɗanda su ne da hannu wajen ƙaruwar rikici a yankin arewa da tsakiyar ƙasar, ba za su yi amfani da wannan turka-turka da ta taso ba.