Coronavirus: An janye dokar takaita zirga-zirgar dare a Mali

Asalin hoton, Agence Afrique
Mahukunta a Mali sun janye dokar takaita zirga-zirga cikin dare da aka sanya a Mali a karshen watan Maris, 2020 domin dakile yaduwar cutar korona a kasar.
To sai dai kuma an wajabtawa kowa a kasar sanya takunkumin fuska musamman idan mutum zai shiga cikin jama'a.
Firaministan kasar, Boubou Cisse, ya yi gargadin cewa cutar ta shiga kusan ko ina a yankunan kasar dan haka ya bayyana bukatar da ake akwai ta kara yin gwaji a kan mutane fiye da a baya.
Mahukuntan kasar sun ce ya zuwa ranar 10 ga watan Mayun, 2020, akwai kasa da mutane 700 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, inda 35 daga cikinsu kuma suka mutu.
Kwararru a bangaren lafiya sun yi gargadin cewa Mali na cikin hadari idan har cutar ta korona ta ci gaba da yaduwa a cikin kasar saboda rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya wanda ke da nasaba da rikicin da aka shafe kusan shekara 10 ana yi a kasar.








