An kashe sojojin Mali fiye da 20 a wani harin kwanton ɓauna

Malian troops take position outside the Radisson Blu hotel in Bamako, Mali on November 20, 2015

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dakarun Mali da goyon bayan sojojin Faransa na yaƙi don murƙushe 'yan ta-da-ƙayar-baya tsawon lokaci

Sojoji a ƙalla 24 ne aka kashe kuma akwai wasu da ba a san halin da suke ciki ba bayan 'yan bindiga sun yi wa kwambar motocinsu kwanton ɓauna a tsakiyar Mali.

Rundunar sojjn ƙasar ta ce an samu soja takwas da suka kuɓuta bayan harin na ranar Asabar, wamda aka kai a wani wuri mai nisan kilomita 100 daga kan iyaka da ƙasar Mauritaniya.

Babu wata ƙungiya da ta amsa cewa ita ce ta kai wannan hari zuwa yanzu amma dai an san 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi suna da ƙarfi a yankin.

Tun a shekarar 2012 Mali ta shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda rashin kwanciyar hankali, lokacin da tawayen masu iƙirarin jihadi ya ɓarke a arewacin ƙasar.

Jami'an soja sun ce kimanin mota 12 ce a cikin kwambar ababen hawan, kuma an lalata huɗu daga cikinsu a wannan harin kwanton ɓauna.

Editan BBC na Afirka, Will Ross ya ce da rahotannin ɓatan sojoji, abu mai yiwuwa adadin waɗanda suka mutu ya fi abin da rundunar sojin ƙasar ke bayyanawa.

Wannan wata asara ce mafi girma ga sojin Mali tun bayan watan Nuwamban bara lokacin da aka kashe sojoji 53 a arewacin Mali.

A ranar Asabar ma, an kashe jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya biyu, lokacin da aka far wa kwambar motocinsu a arewacin ƙasar.

Majalisar Ɗinkin Duniya na da dakaru dubu goma sha uku a Mali.

Tun cikin 2012, dakarun Mali suka ƙoƙarta da taimakon Faransa, suka ƙwace iko da makeken yankin da 'yan ta-da-ƙayar-baya suka karɓe.

Faransa ta tura dakarunta 4,500 zuwa yanki.

Sai dai dubban mutane sun mutu yayin da Mali ke fafutukar shawo kan ayyukan tarzomar, da suka fantsama zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar masu maƙwabtaka.

Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya miƙa tayin hawa teburin tattaunawa da masu iƙirarin jihadi, ko da yake, mai aiko da rahoton BBC na cewa ga alama fatan cewa matakin na iya yin tasiri kaɗan ne.