An kashe sojoji 53 a arewacin Mali

Asalin hoton, Getty Images
'Yan bindiga a arewa maso gabashin Mali sun kashe sojoji 53 da kuma farar hula daya a wani hari da suka kai a wani sansanin sojoji da ke kasar.
A wani sako da rundunar sojin kasar ta aika a shafinta na Twitter, ta bayyana harin a matsayin ''harin ta'addanci.''
Wannan na daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai fiye da shekaru 10 a kasar.
Mali ta fara fuskantar irin wadannan hare-haren tun 2012 bayan da mayaka masu ikirarin jihadi suka samu nasarar kwace ikon arewacin kasar.
Sai dai da taimakon kasar Faransa, sojojin Mali sun yi kokari sun kwato wannan yankin amma duk da haka akwai rashin tsaro.
Irin wannan rikicin ya bazu a wasu kasashe da ke yankin.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Yaya Sangare ya ce sojojin da aka tura domin kai agajin gaggawa ga sansanin bayan harin da aka kai a ranar Juma'a sun gano mutane 10 da suka sha da kyar a harin
Ko a karshen watan Satumba sai dai aka kashe sojoji 38 bayan da aka kai hari ga wasu sansanonin soji biyu da ke kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.
Mali - tare da kasashen Chad da Nijar da Mauritania na daga cikin kasashen da suka kafa wata rundunar hadin gwiwa da taimakon Faransa mai suna G5 Sahel domin yaki da rashin tsaro.
Kasashen guda biyar sun dora alhakin harin da aka kai a watan Satumba ga kungiyar ''Ansarul Islam.''
An kirkiro kungiyar Ansarul Islam ne a 2016 wanda wani mai da'awar jihadi Ibrahim Malam Dicko ne ya kirkirota.











