An kashe sojoji 25 a harin Mali

Malian soldiers stand holding rifles and listening to their national anthem during celebrations to mark the country's independence

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Wannan na daya daga cikin munanan hare-hare da aka kai wa dakarun Mali a wannan shekarar

A kalla sojojin Mali 25 ne suka mutu yayin da 60 suka yi batan dabo bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari a sansanin sojoji biyu, in ji gwamnati.

An kai hare-hare a sansanoni da ke garuruwan Boulkessy da Mondoro kusa da iyakar kasar da Burkina Faso ranar Litinin.

Gwamnati ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindigar 15 kuma tuni suka kwato yankin amma sun rasa kayan aiki da dama.

A yanzu dai dakarun Mali sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da Burkina Faso da dakarun Faransa a yankin.

Mali ta fuskanci mummunan tashin hankalin addini da rikice-rikicen kabila tun shekarar 2012, lokacin da masu ikirarin jihadi suka mamaye arewacin kasar kuma faransa ta kaddamar da sulhu ta hanyar ayyukan soji a yankin.

Wannan dai na daya daga cikin munanan hare-haren da aka kai wa dakarun gwamnati a wannan shekarar.

Kasar tare da Burkina Faso da Cadi da Nijar da Mauritania, na cikin wata kungiya mai yaki da ta'addanci da Faransa ke mara wa baya wadda aka fi sani da G5 Sahel.

Ranar Litinin kungiyar ta zargi "'yan kungiyar Ansarul Islam" da kai harin Boulkessy.

Wani shahararren mai wa'azi Ibrahim Dicko ne ya kafa Ansarul Islam, wanda ke nufin Masu Kare Musulunci, a shekarar 2016.

Rahotanni sun nuna cewa ya yi yaki da masu ikirarin jihadi a arewacin Mali a shekarar 2012.

Map
Presentational grey line