Mutum 38 ne suka mutu a harin Mali

Asalin hoton, Getty Images
Wasu hare-hare da aka kai wasu kauyuka biyu a yankin tsakiyar Mali sun yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 38, ranar Litinin.
Da yawa daga cikin wadanda suka mutu dai 'yan kabilar Dogon ne a garuruwan Gangafani da Yoro.
Hare-haren su ne tashin hankali na baya-bayan nan a jerin rikice-rikicen kabilanci.
Wani rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce, wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta bayyana hare-haren a matsyain na ta'addanci.
A farkon watan nan ne mutum 35 da suka mutu a lokacin da aka kai hari a kauyen Dogon da ke Sobame Da.
A watan Maris, sama da Fulani 130 ne 'yan bindiga sanye da kayan maharban gargajiya na Dogon suka kashe, a wani kauye duk dai a yankin tsakiyar Mali.
Wannan ya ja har Shugaban Malin, Boubacar Keita ya kori babban kwamandan sojojin kasar.
A watan Yuni, wasu mutane dauke da makamai sun afka wa garin Dogon na kasar Mali, inda suka kashe kusan mutum 100.
An kai wannan hari ne a Sobane-Kou kusa da garin Sanga. Maharan sun kuma cinna wa gidaje wuta, inji wadanda suka shaida al'amarin.
Shugaba Keita ya yi kira da a kawo karshen wadannan tashe-tashen hankula, sai dai mutane na sukar gwamnatin kan gazawarta wajen kawo karshen rikice-rikicen.











