Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Afirka: Adadin masu cutar a nahiyar ya zarce miliyan ɗaya
Adadin masu cutar korona a nahiyar Afrika ya zarta miliyan ɗaya, kamar yadda ƙididdiga daga Jami'ar Johns Hopkins da ke bin diddigin annobar korona a Afrika ya nuna.
Adadin na ranar Alhamis ya nuna mutum 1,007,395 ne suka kamu da cutar tun da ta bayyana a watan Fabrairun wannan shekarar.
Ƙasar Afrika ta kudu ke kan gaba a yawan masu cutar a nahiyar da mutum 538,184.
Sai ƙasar Masar da ke da mutum 95,006, inda Najeriya ke mataki na uku da mutum 44,890.
Jadawalin ya kuma nuna Ghana na da mutum 39,642, sai Aljeriya mai mutum 33,626, sai kuma Moroko mai 29,644.
Mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar a nahiyar Afrika ya fito ne daga Masar, inda aka tabbatar da hakan tun a ranar 14 ga watan Fabrairun 2020
Tun bayan ɓullar cutar a nahiyar, ƙididdiga a ranar ta Alhamis ta nuna cewa cutar ta kashe sama da mutum 22,059 a nahiyar, haka kuma mutum 690,011 suka warke bayan sun kamu da cutar a baya.
Ƙididdigar ta kuma tabbatar da cewa mutum 22,062 ne suka mutu sakamakon cutar a faɗin nahiyar ta Afrika
Yadda lamarin yake a wasu sassan duniya
Ƙasashe ƙalilan ne annobar korona ba ta leƙa ba, kuma da alama ta fi yin ta'adi a wasu ƙasashen kawo yanzu.
A halin da ake ciki, Amurka ce ke kan gaba wajen yawan masu fama da cutar, inda mutum 4,876,790 suka kamu, sai Brazil mai mutum 2,912,212.
Alƙaluman da hukumomin Indiya suka fitar na cewa fiye da mutum miliyan biyu ne suka kamu da cutar.
Ƙasar ta sami wannan tashin goron zabin daga mutum miliyan daya zuwa miliyan biyu ne cikin kwana 20 kacal.
Cikin awa 24 da suka gabata, Indiyawa 62,170 ne suka kamu da cutar, wanda ya sa adadin masu fama da Covid-19 kai wa 2,025,409.
A nahiyar Turai kuwa ƙasashen Rasha da Sifaniya da Birtaniya da kuma Italiya ne ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar.
Rasha na da mutum 870,187, Sifaniya na da mutum 309,855, inda ƴan Birtaniya 309,784 ne suka harbu.
Daga nahiya zuwa nahiya...
Idan aka kwatanta yadda lamarin ya kasance tsakanin nahiyoyi kuwa, ko shakka babu nahiyar arewacin Amurka ce ke kan gaba:
- Kasashe 39 ciki har da Canada da Amurka da Mexico da wasu ƙananan ƙasashe da tsibirai da adadinsu ya kai ƙasa 39, suna da masu cutar korona 5,912,180.
- Nahiyar Asia mai ƙasashe 49 ciki har da China da Indiya da Iran da Saudiyya da Pakistan da kuma Bangladesh na da mutum 4,774,302.
- Nahiyar kudancin Amurka mai ƙasashe 14 na da mutum 4,534,206.
- Nahiyar Turai mai kasashe 48 na da mutum 2,982,576.
- Nahiyar Afirka mai ƙasashe 57 na da 1,011,463.
- Sai kuma nahiyar Oceania ma kasashe shida da suka hada da Ostreliya da New Zealand da Papua New Guinea da French Polynesia da Fiji da kuma New Caledonia na da mutum 21,735 ne kawai.
Ƙasashen da suka fi gudanar da gwaje-gwajen masu cutar korona
Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha bayyana cewa yin gwaje-gwaje ita ce hanya mafi dacewa wajen gano masu cutar cikin al'umma.
Zuwa ranar 5 ga watan Agusta, China ta gwada ƴan ƙasarta fiye da miliyan 90.
Amurka ce ƙasar da ke bi ma China. Ta gwada fiye da mutum miliyan 61 da rabi.
Rasha ce ta uku da mutum fiye da miliyan 29, Indiya kuma ta gwada fiye da mutum miliyan 21 kawo yanzu.
Birtaniya ta gwada fiye da mutum miliyan 16, Brazil kuwa na da mutum kusan miliyan 13 da rabi da ta gwada.
Sauran kasashen da ke ƙoƙarin gwaje-gwaje:
Jamus miliyan takwas, Sifaniya miliyan bakwai sai Italiya fiye da mutum miliyan shida. Turkiyya da Canada kuwa na da fiye da mutum miliyan huɗu-huɗu tsakaninsu da suka gwada.
Saudiyya da Afirka ta Kudu kuwa sun gwada fiye da mutum miliyan uku-uku.
Amma a Najeriya, hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa, NCDC ta ce ta gwada mutum 306,894 ne zuwa ranar Alhamis 6 ga watan Agusta.
Ƙasashe biyar da aka fi mutuwa daga cutar korona
- Amurka - 162,780
- Brazil - 98,644
- Mexico - 49,698
- Birtaniya - 46,413
- Indiya - 41,638
Ƙasashe biyar da aka fi warkewa daga cutar korona
- Amurka - 2,575,986
- Brazil - 2,047,660
- Indiya - 1,377,384
- Rasha - 676,357
- Afirka ta Kudu - 387,316