Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Abubuwan da har yanzu ba mu sani ba kan cutar
- Marubuci, Daga James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Lafiya da Kimiyya
A watan Disambar bara duniya ta san da coronavirus, amma yadda ta kankane duniya, sai a ga kamar ta dade da bayyana.
Duk da matukar kokarin da masana kimiyya ke yi a fadin duniya, akwai abubuwa da dama da har yanzu ba mu fahimta ba, kuma a yanzu, dukkanmu mun zama wani bangare na gwaji a fadin duniya wajen gano amsoshi.
Ga wasu daga cikin manyan amsoshi dangane da wannan cuta.
1. Mutum nawa ne suka kamu
Wannan ita ce tambayar da aka fi yi, kuma daya daga cikin tambayoyi masu muhimmanci.
An tabbatar da kamuwar dubban mutane da cutar a fadin duniya, amma wannan dan bangare ne kawai na gaba daya mutanen da suka kamu a duniya.
Kuma akwai dumbin mutane da ba su nuna alamomin cutar amma suna dauke da ita- wannan na kara rikita alkaluma.
Samar da gwajin 'antibody' wato sinadaren da ke cikin jini, zai bai wa masu bincike sani idan mutum na dauke da kwayar cutar.
Ta yin haka ne kawai za a fahimci yadda cutar ke yaduwa.
2. Munin ta
Idan ba a san yawan mutanen da ke dauke da cutar ba, babu yadda za a yi a gano yawan mutanen da take kashewa.
A halin yanzu, kiyasin shi ne kusan kaso daya cikin 100 na mutanen da ke dauke da cutar ke mutuwa.
Amma idan akwai, mutanen da ke dauke da cutar kuma ba sa nuna alamominta, wato bata bayyana a jikinsu karara ba, yawan mace-macen na iya raguwa.
3. Cikakkaun alamominta
Manyan alamomin coronavirus su ne zazzabi da tarin da bai zuwa da majina- wadannan ne ya kamata a lura sosai a kansu.
Wasu mutanen sun ce sun fuskanci ciwon wuya da ciwon kai da gudawa, kuma ana tunnain wasu kan kasa shaker kamshi.
Amma tambaya mafi muhimmanci ita ce ko wasu na fuskantar alamomin mura kamar zubar majina ko atishawa.
Bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar haka kuma mutane na iya yada cutar ba tare da sun san cewa suna dauke da ita ba.
4. Rawar da yara ke takawa wurin yada ta
Tabbas yara na iya kamuwa da coronavirus. Amma ba ta cika wahalar da su ba kuma ba ta cika kashe su ba idan aka hada da sauran mutane.
Yara na kan gaba wajen yada cutar, babu mamaki saboda suna cudanya da mutane masu yawa (musamman a wurin wasa), amma idan ana batun wannan cutar, babu tabbas kan girman yadda suke taimakawa wajen yada ta.
5. Inda ta fito
Cutar ta fito ne daga Wuhan a China a karshen shekarar 2019, inda aka gano wasu masu dauke da ita a wata kasuwar sayar da nama.
Coronavirus, wadda a hukumance ake kiranta Sars-CoV-2, na da alaka ta kusa-kusa da wasu cutuka da ke shafar jemagu, sai dai ana tunanin ita wannan cutar jemagun ne suka shafa wa wata dabba da ba a gano ko wace iri ba ce, ita kuma ta shafa wa mutane.
Har yanzu dai ba a gano takamaimai asalin dabbar ba, don haka tana iya ci gaba da yada wa mutane cutar.
6. Masu dauke da cutar za su ragu a lokacin bazara
An fi yin mura a lokacin sanyi maimakon a lokacin zafi, amma har yanzu ba a sani ba idan lokacin zafi zai shafi yaduwar cutar.
Masu bai wa gwamnatin Burtaniya shawara kan kimiyya sun yi gargadin cewa kawo yanzu, ba su sani ba idan yanayi zai shafi cutar.
Idan aka samu ragi a yaduwar coronavirus lokacin zafi, akwai hadarin za a samu karin yaduwarta a lokacin sanyi, lokacin da asibitoci ke fama da yawan marasa lafiya da ke mura.
7. Abin da ya sa cutar ta fi wahalar da wasu
Ga mutane da yawa, covid-19 ciwo ne mai sauki. Amma cutar kan zama mai muni ga kusan kashi 20 cikin 100 na mutane. Ko me ya sa?
Matsayin garkuwar jikin mutum na iya zama dalili, haka kuma akwai wasu abubuwa a jiki da mutum ke gada daga iyayensa da ke taka rawa.
Fahimtar wannan na iya samar da hanyoyin kare mutane daga shiga mawuyacin hali.
8. Tsawon lokacin da garkuwar jiki ke iya kare mutum daga kamuwa, kuma idan ana iya yin cutar sau biyu
Ana ta ce-ce-ku-ce kan yadda karfin garkuwar jiki ke iya kashe cutar amma babu wata shaida da ta nuna hakan.
Idan har masu dauke da cutar suka warke, to hakan na nufin garkuwar jikinsu ta gina matakan yaki da cutar.
Amma da yake cutar ba ta dade ba, babu wasu bayanai masu yawa.
Ana jita-jitar cewa akwai mutanen da cutar ke kamawa sau biyu, kuma babu mamaki an samu wannan ne saboda an yi gwajin ba daidai ba.
Batun garkuwar jiki na da muhimmanci a fahimtar abin da zai faru nan gaba.
9. Idan cutar za ta sauya fasali
Kwayoyin cuta na 'virus' na sauya fasali ko yaushe, amma sauye-sauyen da ke faruwa ga asalin kwayoyin halittarsu ba shi da yawa.
Ana sa rai kwayoyin cuta su sauya su rage karfi nan gaba, amma babu tabbacin haka.
Fargabar ita ce idan coronavirus ta sauya, garkuwar jiki ba za ta gane ta ba kuma riga-kafinta ba zai kare mutane daga kamuwa da ita ba.