Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
Coronavirus na ta ci gaba da yaduwa da kashe mutane a duniya, amma dai abin dadin shi ne yawan wadanda suke warkewa ya fi yawan wadanda suke mutuwa.
To mece ce coronavirus, ta yaya take yaduwa kuma a wane mataki ne za a gane ta fi kama mutum?
Ta yaya zan kare kaina?
Abin da ya fi kamata a yai shi ne yawan wanke hannu da ruwa da sabulu.
Coronavirus tana yaduwa ne idan mutum da ke dauke da ita ya yi tari har kwayoyin cutar suka yadu a cikin iska.
Da zarar wani ya shaki isakar ko kuma ya taba wajen da kwayoyin cutar suka fada akai, sannan ya taba idonsa ko hancinsa ko bakinsa, to zai iya kamuwa.
Don haka yin tari da atishawa a cikin toli fefa, da gudun taba fuskarku da hannayen da ba a wanke ba, da kuma gujewa yin alaka ta kut da kut da mutanen da suka kamu na da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cutar.
Kwararru a fannin lafiya sun ce takunkumin rufe fuska ba ya tasiri sosai wajen kariya.
Mene ne alamun coronavirus?
Coronavirus na shafar huhu. Alamun na farawa ne da zazzabi sai tari mai zafi ya biyo baya, wanda ke iya jawo matsalar numfashi.
Wannan sabon abu ne, tari mai naci da za a yi ta yi har fiye da sa'a daya, ko kuma yin tari a jejjere kamar sau uku cikin sa'a 24, (idan ka saba yin tari to wannan za ka ga ya fi na yadda ka saba).
Yana daukar kwana biyar kafin alamun su fara bayyana, kamar yadda masana kimiyya suka ce, amma wasu mutanen su kan nuna alamun bayan fiye da kwana biyar din.
A takaice dai Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce a kan dauki kwana 14 kafin cutar ta gama bayyana.
Mutane sun fi saurin yada cutar idan sun fara nuna alamunta, amma kuma wasu na iya yada ta tun ma kafin alamunta su fara bayyana.
Alamun farko-farkon suna iya rudar da mutum ta hanyar kamanceceniyar da suke yi da irin murar da aka saba.
Yaya munin coronavirus yake?
Hasashe yana nuna cutar ba ta kisa sosai, tana kashe kashi 1 zuwa biyu cikin 100 - amma wannan hasashe ba shi da tabbas.
Ana ci gaba da bai wa dubban mutane kulawa a asibiti, amma akwai yiwuwar da yawa su mutu. Amma kuma akwai yiwuwar mace-macen ba zai yi yawa ba idan ana samun masu dauke da cutar da ba ta yi tsanani ba.
Bayanan Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO daga marasa lafiya 56,000 da aka samu sun nuna cewa:
Kashi 6 cikin 100 na yin rashin lafiyar da tsananin - huhu ya daina aiki, matsarmama ta daina aiki, da kuma barazanar muutwa
Alamun cutar na bayyana sosai ga kashi 14 cikin 100 - wahala wajen shan numfashi da daukewar numfashi
Kashi 80 cikin 100 ne ke yin rashin lafiyar saisa-saisa - zazzabi da tari, sai kuma wasu suna kamauwa da lumoniya