Coronavirus a duniya: Yaya takunkumi yake shafar yadda muke hira?

Wasu abokan zama biyu na sanye da takunkumi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idanunmu da bakunanmu sun fi komai muhimmanci a fuskokinmu
    • Marubuci, Daga Sandy Ong
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future

A yau, sama da kasashe 50 a fadin duniya sun mayar da sanya takunkumi a bainar jama'a, wajibi.

Wasu 'yan kasashe da dama na sanya takunkumin a duk inda suka samu kansu da nufin kare kansu da kuma wasu daga kamuwa daga cutar korona.

A wasu kasashe da dama, musamman a nahiyar Asiya, akan sanya takunkumi saboda neman kariya daga gurbatar iska ko kuma sanyin gari - kuma wannan wani abu ne da aka saba da shi tun kan zuwan wannan annoba.

Amma a kasashen da suka fara amfani da shi yanzu wasu na ganin abu ne mai wahalarwa mutum ya yi ta yawo da takunkumi.

Darasin da za mu iya dauka daga sanya takunkumi

Kungiyoyin ba da agaji sun yi gargadin masu fama da kurumta da dangin matsalar ji, za su fuskanci matsi idan sanya takunkumi ya zama ruwan dare a fadin kasashe.

Amma miliyoyin mata a fadin duniya na sanya mayafi kullum ba tare da fuskantar matsalar a-zo-a-gani ba wajen maganganunsu.

Wata mata sanye da takunkumi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane a fadin duniya na sanya takunkumi domin kare kansu daga cutar korona.

Abu ne da ke bayyane, cewa takunkumi ya sha bamban daga muhimmancinsa da yadda yake kare fuska kamar nikab ko burka. Sai dai shi takunkumi ana sanya shi ne saboda dalili na lafiya shi kuma nikab ko burka al'ada ce sanya shi a wajen Musulmai.

Duka kayan kariyar biyu na da ma'ana daban da kuma dalilan sanya su ga masu sa wa.

Me za mu iya koya a wajen mata da ke sanya gyale don kare fuskokinsu kan yadda suke magana yadda ya kamata? Da kuma yadda takunkumi ke kawo koma baya wajen harkokinmu na yau da gobe?

"Mutane sun fi mai da hankali kan fuska maimakon siffar mutum baki daya," in ji wata masaniyar halayyar dan adam Rebecca Brewer, wadda ta karanci rawar da gabban jikin dan adam ke takawa wajen isar da sako ko kuma hira a jami'ar Royal Holloway da ke London.

"Lokacin da ba ma iya ganin fuskokinmu irin wadannan alamun sai su bace bat"

Muhimmancin fuska da baki lokacin maganar ta hanyar ishara

Lokacin da ake karantar fuska ido da baki su ne yankuna mafi fayyace bayanai saboda sun fi bayyana abin da ke zuciya.

Kowacce gaba za ta iya fitar da bayani na musamman da ake bukata. Kamar bangaren baki ya fi kyau wajen bayyana jin dadi da farin ciki.

Wani buɗaɗɗan baki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Garƙame baki kan zama matsala lokacin da muke da niyyar nuna farin ciki ga abokanmu

Garƙame baki kan zama matsala lokacin da muke da niyyar nuna farin ciki ga abokanmu - wanda ke bayyana dalilin murmushin ma'aikatan lafiya yayin aiki domin samar da nutsuwa a zuciyar marasa lafiya da suke cikin damuwa.

Amma dogara a kan fuska ko kuma wasu hanyoyin kan iya zama guguwar fahimta, dole sai an kula in ji Aleix Martinez, wani farfesa kan sha'anin kwafuta da lantarki a jami'ar Ohio da ke Amurka.

Lokacin da murmushi kan zama na bogi

Martinez yana karantar yadda za mu iya gane bayanan ta hanyar motsa jiki dan a koyawa na'ura ta rika yi kamar dan adam.

"Kar mu zama muna farin ciki da murmushin mutane, kar kuma mu rika murmushi duk lokacin da muke cikin farin ciki," ya kara da cewa.

A takaice bincike ya nuna a kwai nau'in murmushi 19 - kuma shida ne kawai ke da alaka da murna da farin ciki. Sauran muna yi ne lokacin da muka tsorata, ko muka wulakanta ko muka ji raɗaɗi da dai sauran dalilai.

Wani magoyin baya na murnan cin kwallo a Afrika ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A iya cewa motsin jiki kan iya zama na bogi, in ji masana. wannan shi ne yadda ake murnar cin kwallo a lokacin wasa

Domin ba da hujja ga abin da ya fada, Martinez ya nuna hotuna biyu, daya wata matshiya fuskarta a turɓune, hawaye na zuba a idonta, a bangare daya kuma wani mutum mai jan ido da bakinsa bude da ke nuna alamun ihu.

Ta yi kamar tana cikin mummunan ɓacin rai shi kuma kamar zai kashe wani, in ji Martinez. Amma lokacin da ka yi masa kallon tsanaki za ka fuskanci yana cikin tsananin murnar cin kwallo ne.

A irin wannan yanayin fuska ba ta nuna abin da ke cikin zuciya ba.

Samar Al Zayer, da ke zaune a Netherland wadda kwararriyar masaniyar halayyar dan adam ce ta gano wannan gaskiya a zamanta da ta yi a Saudiyya.

Lokacin da ita kanta ba ta rufe fuskarta, amma mafi yawan 'yan uwanta na sanyawa.

Bambanci

"Na dan san kadan daga cikin yadda suke zancensu ba ta hanyar furta kalmomi ba, ta yadda ake tsira ido sosai don gane me ke damunsu, tare da fahimtar halin da suke ciki. Ina lura da yadda sautinsu ke futa da kuma yadda hannuwansu ke motsawa," in ji Zayer.

"Ba kawai jin bambancin ake ba abu ne da ke a bayyane".

Wasu mata sanye da gyale

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanya gyale ba ya hanasu jin magana ko kuma isar da sakon da ya kamata a lokacin da ake da bukatar hakan

Maria Ali mai shekara 34 a Rawalpindi da ke Pakista tana sanya nikab kuma ta ce ba ta taba samun matsala ba wajen yin magana da masu niƙab irinta ba a duk lokacin da take so, ko da kuma baki ne.

"Daga yadda suke motsa hannuwansu da jikinsu za ka gane me suke nufi," in ji ta

Sauran bangaren idon da zai kasance a waje ko da akwai niqab zai iya bayyana abin da ke zuciya. Katambayi Shakespear wanda ya rubuta "Idanu kamar taga ne a wajen rai".

Shakespeare

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shakespeare ne ya rubuta wannan littafi

Masana halayyar dan adam sun ce akan gane halin da kwakwalwa ke ciki - damuwa da yakini da bukata da niyya da dai sauransu ta cikin idanu ta wani "ra'in fahimtar zuciya".