Coronavirus a Najeriya: Wacce rawa masu haƙar kabari ke takawa a yaƙi da annobar korona?

Makabarta a Kano

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu hakar kabari a Kano sun ce sun binne mutane fiye da yadda suka saba a baya a jihar
    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Daya daga cikin abubuwa da ake gani yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar korona ita ce matukar karuwar kaburbura a makabartu - inda a wasu wuraren makabartu kan cika makil har ana binne mamata da dama a kabari daya, misali, a kasashen Amurka da Brazil.

A wasu wuraren, kamar a arewacin Najeriya musamman jihar Kano, masu aikin hakar kabari ko kula da makabartu, sun yi batun cewa aiki ya kara yi musu yawa a wannan lokaci na annoba - lamarin da ya kasance babban kalubale a gare su.

A wasu lokuta kuma bayanan da ake samu daga masu kula da makabartu ka iya yin karin haske kan adadin mutane da ke mutuwa yayin da ake kokarin dakile cutar ta korona mai kisa.

Kawo yanzu Najeriya ta tabbatar da samun mutane 16,658 da suka kamu da cutar cikinsu kuma 424 sun mutu.

Makabarta
Short presentational grey line

Karuwar mace-mace a arewacin Najeriya

A watannin baya-bayan nan - musamman daga watan Maris zuwa farkon watan Mayu - an samu rahotannin karuwar mace-macen mutane musamman wadanda suka manyanta a wasu jihohin arewacin Najeriya kamar Kano da Jigawa, da Bauchi da Yobe da sauransu.

Daruruwa ko ma dubban mutane ne suka rasu a yankin a cewar rahotanni inda a jihar Kano kadai binciken hukuma ya nuna cewa mutane kusan 1000 suka mutu cikin kimanin wata guda, wato daga farkon watan Afirilu zuwa farkon watan Mayu.

Wannan al'amari ya haifar da damuwa matuka, da kuma fargabar cewa kila cutar korona ce ke kisan mummuke - musamman ganin an samu yawan mace-macen ne a lokacin da ba a cika yin gwaje-gwajen cutar a arewacin Najeriya ba saboda rashin cibiyoyin gwaji a yankin, kuma da dama daga cikin wadanda suka mutu, sun nuna alamomi masu kama da na cutar korona gabanin mutuwarsu.

Matsalar yawan mace-macen ta kai ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa dokar kulle a jihar ta Kano kafin daga bisani aka sassauta dokar.

Short presentational grey line

Masu kula da makabartu ne dai suka fara fito da maganar fili ta hanyar hirarraki da kuma ta kafofin watsa labarai, bayan da suka lura da matukar karuwar yawan gawawwakin da ake kawo masu domin jana'iza a kullum.

A wasu makabartun an bada lamarin cewa a kullum akan binne gwamman gwawwaki, kuma wannan lamari ne da ba a saba ganin irinsa ba kafin zuwan annobar korona.

Bayanai daga makabartun, wadanda kafofin labarai suka wallafa, sun taimaka wajen jawo hankalin hukumomi da kuma matsa masu lamba wajen tashi tsaye domin bincika lamarin da kuma gano gaskiyar abin da ke faruwa.

Wani mai aikin hakar kabari, mai suna Ali, ya shaida wa BBC cikin watan Afirilu cewa "ba mu taba ganin irin wannan yanayi ba."

Ya ce rabuwarsu da irin wannan yawan mace-mace tun lokacin wata gagarumar annobar kwalara da aka yi kimanin shekaru 60 da suka wuce.

A cewarsa iyayensu sun ba su labarin cewa a lokacin wasu har gudu su ke yi idan aka ce ga mutane sun mutu su zo su yi aikin jana'iza saboda yawan aikin da kuma tsoron kamuwa da ciwo.

Binciken yawan mace-mace masu nasaba da korona a Najeriya

Gwamna Ganduje

Asalin hoton, KNSG

Bayanan hoto, Kashi 50 zuwa 60 na mutum kusan 1,000 da suka mutu a Kano, korona ce ta yi ajalinsu

Da farko dai hukumomi musamman na jihohin da aka samu karuwar mace-macen mutane, sun nuna shakku kan cewa annobar korona ce ke haddasa karuwar mace-macen mutane musamman wadanda suka manyanta a daidai lokacin da ake fama da annobar cutar.

Amma daga bisani gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti domin binciken lamarin.

Daga karshe kwamitin ya bayar da sakamakon aikinsa kan matsalar yawan mace-mace a jihar Kano, wanda ya ce na da nasaba da annobar korana.

Minsitan lafiya na Najeriya Dokta Osagie Ehanire, ya shaida wa manema labarai cewe kwamitin ya gano an samu mutuwar mutane 979 a birnin Kano a a tsawon kimanin makwanni biyar - wato a cikin watan Afirilu da kuma farkon watan Mayu.

Ministan ya ce binciken ya gano cewa kimanin kashi 50 zuwa kashi 60 cikin 100 na mace-macen, ga alama cutar korona ce sanadinsu. Wannan yana nufin kila cutar korona ta yi ajalin mutane fiye da 500 a jihar Kano kadai.

Minista Osagie Ehanire ya ce a tsakiyar watan Afirilu lokacin da adadin mace-macen a Kano ya kai kololuwa, akan samu mutuwar akalla mutane 43 a duk rana, kafin daga bisani a cikin watan Mayu al'amarin ya kyautata, aka samu raguwar mace-macen kuma adadin ya koma kamar yadda aka saba gani gabanin annobar wato kimanin mutum 11 a kullum.

Sakamakon binciken dai ya sanya mutane da dama na ganin hakikannin barnar da cutar korona ke yi a kasar ta fi yadda hukumomi ke bayyanawa a alkaluman da suke bayarwa na yau da kullum, ya kuma kara nuna muhimmancin bukatar da ake da ita ta bunkasa ayyukan gwaje-gawjen cutar a fadin kasar mai mutume kimanin muliyan 200.

Kawo yanzu dai ba a bayyana sakamakon binckken wasu jihohi da aka samu karuwar mace-mace ba. Kwamitin dai ya ziyarci jihohi da dama a arewacin Najeriya inda aka samu rahotannin karuwar mace-mace.

Kwamitin ya ce masu kula da makabartu sun taimaka masa kwarai wajen samun bayanai da kara fahimtar lamuran da ke faruwa ta yadda aka dauki matakan da suka dace wajen tunkarar matsalar ta mace-mace wadanda wasunsu na da nasaba da cutar korona.

Wani mai aikin hakar kabari a Kano mai suna Abubakar, ya ce sun taimaka wa kwamitin binciken da bayanai a yayin binciken. Ya kara da cewa ''yanzu babu wannan matsala ta yawan mutuwa, Allah Ya kawo mana sauki. Alhamdulillahi''

Shugaban kwamitin Dokta Nasiru Sani Gwarzo ya ce masu kula da makabartu na taimakawa a yunkurin da ake yi wajen yaki da korona.

Ya ce masu ginar kabarin, sun bayar da bayanai kan yanayin mace-mace, da alkaluman mace-mace, da adireshin mamata abin da ya taimaka wa 'yan kwamitin suka samu damar zuwa wasu daga cikin gidajen da aka yi mace-mace suka gudanar da bincike.

Short presentational grey line
DR NASIRU GWARZO
Bayanan hoto, Dr Gwarzo masu ginar kabarin sun bayar da bayanai kan yanayin mace-mace
Short presentational grey line

Dr Gwarzo ya ce yadda masu kula makabartu suka taimaka ya burge su matuka - inda ya bayar da misali da yadda suka tarar da ma'aikata a babbar makabarta dake Azare, jihar Bauchi, sun tanadi wani kyakkyawan tsararren kundin bayanan mace-mace, abin da ya saukaka masu nasu aikin binciken.

Galibin wadanda suka mutu a jihohin da aka yi fama da matsalar karuwar mace-macen dai, a gida suka rasu - ba a asibiti ba - kuma dama Najeriya na da matsala ta tattara alkaluma kan al'umarta.

Don haka kwamitin ya dogara kan masu kula da makabartu domin samun bayanai, kana ya tuntubi 'yan uwan mamatan, abin da ya kara nuna muhimmancin masu kula da makabartu a yaki da cutar korona.

Masu kula da makabartu na cikin matukar hadarin kamuwa da korona

Ko shakka babu, aikin hakar kabari da kuma binne gawa, aiki ne mai hadarin gaske. Akwai matsalar jin rauni da ta kamuwa da cututtuka. Masana na ganin hadarin yakan karu matuka a irin wannan lokaci na annobar cututtuka masu yaduwa kamar korona.

Da ma masana lafiya sun yi gargadin cewa mutane wadanda ba kwarraun ma'aikatan lafiya ba su guji taron jana'iza ko taba gawa a iirn wannan lokaci don gudun kamuwa da cutar ta korona.

Shugaban kwamitin da ya gudanar da bincike kan yawan mace-macen na arewacin Najeriya, Dr Nasiru Sani Gwarzo, ya ce ko da ya ke masu kula da makabartu za su iya ci gaba da gudunar da muhimmin aikin nasu na hakar kabari da kuma daukar bayanan mamata, to amma bai kamata a bar su, su rika taba gawa ko likkafani ba a wannan lokaci na annobar korona.

Kwararrun ma'aikatan lafiya da sauran wadanda aka bai wa horo kan binne gawa, su ya kamata su rika binne mamaci kamar yadda Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya NCDC ta zayyana.

Short presentational grey line

A cewar Dokta Gwarzo, su ma masu aikin hakar kabari, kamata ya yi a ba su horo kan yadda za su kare kansu, a samar masu da tufafin kariyar lafiya a wannan lokaci na korona muddin za su yi wani aiki da ya shafi gawa kai tsaye.

Wannan yana da muhimmanci saboda za su iya kamuwa da cutar korona da ma duk wata cuta mai saurin yaduwa kamar Lassa da Ebola idan ba su dauki matakan kariya ba.

Muddin suka kamu da cutar kuma, za su iya yadawa ga wasu na kusa da su - ciki har da iyalansu. Wasu daga cikin masu aikin hakar kabari, sun shaida wa BBC cewa kawo yanzu Allah Ya kare su daga cutar ta korona.

Short presentational grey line

Aiki mai matukar wahala amma babu albashi

Aikin hakar kabari, ba aiki ne mai sauki da kuma dadi ba - aikin karfi ne da akan yi a lokacin matukar bakin ciki, ba dare ba rana, ba rani da damina.

Haka nan kuma masu hakar kabari su na cikin gata na karshe ga dukkan mai rai babba da yaro - imma talaka ko kuma attajiri ko mai mulki - saboda hidimar da suke yi wajen sanya mamaci a makwanci.

Duka wannan baya ga gudummowar da su ke bayarwa ne a irin wannan lokaci na annobar korona wadda ke janyo mace-macen mutane.

Sai dai kuma, ga alama ba a cika daukar aikinsu da muhimmancin da ya kamata ba - sai idan ta baci.

A zantawar da na yi da wasu masu aikin kula da makabartu, wadanda galibi suka bukaci a sakaya sunayensu, sun shaida mani cewa ko da ya ke suna alfahari da aikin nasu, kuma ba su jin kasalar yi, to amma fa albashi ko kudin alawus da ake ba su bai taka kara ya karya ba.

Kalilan daga cikinsu albashinsu ya kai kimanin N40000 a wata.

Amma galibinsu, ko kusan hakan ba su samu. ''Wallahi alawus da ake ba ni a wata N5000 ne, wani lokaci ma ba ya samuwa a kan lokaci'', in ji wani mai aikin hakar kabari a Najeriya.

Ya kara da cewa wasu masu aikin hakar kabarin ma ba a biyansu ko kobo, illa sukan dogara kan sadaka da wasu daga cikin al'uma ko kuma dangin mamaci ke ba su, duk da cewa da damansu na da nauyin kula da iyali ko na iyaye a kansu.

Sabanin a kasashe da suka ci gaba inda ake hakar kabari da na'ura, a Najeriya masu aikin ginar kabari da hannu suke aiki ta hanyar amfani da diga, da cebur da gatari ko fartanya da kuma wilbaro domin debo kasa da bulo ko kuma tsingaro - wato fasassun tukwane ko kasake.

Dokta Gwarzo ya ce rashin bai wa masu hakar kabari albashi yadda ya kamata, kamar "an raina aikinsu ne. Misali a ce ka haka kabari 45, 50 ko 60 a rana guda, a wasu wuraren ma a tsandauri, ai wannan ba karamin aiki ba ne. ''

Ko da ya ke wasu daga cikin masu kula da makabartun na cewa ba a kula da su yadda ya kamata, to amma sau da yawa sukan kalli aikin nasu ta fuskar addini amma ba ta tattalin arziki ba.

Short presentational grey line

Suka ce abin da ke kwantar masu da hankali shi ne sun yi imanin ladansu na wajen Allah - amma ba batun tattalin arzki a duniya ba, kuma aikin yana kara masu imani da tausayi ganin a kullum suna cikin hidima da ta shafi mutuwa.

Ko baya ga Najeriya, a wasu daidaikun kasashe masu tasowa, masu aikin ginar kabari na kokawa. Misali a kasar Mexico, wani mai aikin hakar kabari ya ce 'ba a martaba aikin masu hakar kabari, an yi watsi da mu''

Haka nan a kasar Somalia, wakiliyar BBC a Mogadishu Bella Sheegaw, ta ce duk da cewa suna aiki cikin tsananin zafin rana a wannan lokaci na korona, kuma suna taimaka wa wajen bayar da bayanai ga hukumomi kan mace-mace da ake fuskanta, to amma masu hakar kabari na fama da karancin albashi da rashin daraja aikinsu yadda ya kamata.

Sai dai ta ce yanzu sakamakon bullar cutar korona lamarin na sauyawa, inda ake samun karin mutane da ke martaba aikin na masu hakar kabari, da kuma ganin daraja da muhimmancinsu.

Masu lura da lamura na ganin kamata ya yi a inganta aikin masu kula da makabartu a kasashe masu tasowa irin su Najeriya domin ya dace da zamani, musamman ta fuskar kayan aiki, da albashi da kuma kundin adana bayanan mace-mace da ake yi a cikin al'uma, kuma a kara martaba su da aikin nasu saboda gagarumar gudummowa da suke bayarwa, ba a lokacin annoba kawai ba, a'a, har ma a kowane lokaci.

Karin labarai da za ku so ku karanta: