Buhari ya ce za a yi bincike kan mace-macen Kano

Asalin hoton, AFP
Shugaban Najeriya ya bayyana damuwa kan mace-macen da aka samu a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar kan annobar cutar korona a ranar Litinin da daddare.
Shugaban ya ce ya aika da tawaga domin gudanar da bincike tare da kulle jihar na tsawon mako biyu.


Kalaman shugaban na zuwa bayan yawan mace-macen da ake samu a Kano fiye da kowane lokaci a baya.
Al'ummar jihar na cikin hali na rashin tabbas kan abin da ya haifar da mace-macen yayin da ake cikin wannan yanayi na annobar korona.
Wasu na tunanin cutar korona ce ta shiga al'umma kuma take yi wa jihar illa.
A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru sun kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin birnin.
Amma hukumomi a jihar sun ce mace-macen da aka samu ba shi da alaka da cutar korona. Sun ce cutuka kamar hawan jini da ciwon suga da sankarau da zazzabin maleriya na iya haifar mace-macen.
Kano ita ce ta uku cikin jerin jihohin Najeriya da ke fama da cutar korona.











