Coronavirus a India: Yadda cutar korona ta haifar da ƙarancin audugar mata

A yayin da ake bikin ranar kula da tsaftar mata lokacin al'ada ta duniya, mun sake wallafa wannan makala da muka soma bugawa ranar 24 ga watan Mayun, 2020.
'Yan matan da ke zuwa makaranta a Indiya na fama da matsanancin ƙarancin audugar mata, saboda makarantu a kasar na cikin jerin masu haƙƙin samar da ita, kuma a yanzu duka an rufe su saboda cutar korona.
Wannan ya jefa miliyoyin 'yan mata a fadin kasar cikin halin damuwa, kamar yadda wakiliyar BBC Geeta Pandey ta ruwaito daga birnin Delhi.
Shekaru da yawa a baya, Priya ta saba karbar fakitin audugar mata goma kowanne wata daga makarantarta.
Yarinya ce 'yar shekara 14 da ke rayuwa a Badli, wani yanki mai matukar cinkoso a arewa maso yammacin Delhi,
Tana zuwa makarantar gwamnati inda ake bai wa dalibai mata audugar kyauta, a wani matakin gwamnatin kasar na karfafa tsaftar mata yayin jinin al'ada.
Wannan ba karamin ƙoƙari ba ne da gwamnatin kasar ke yi, wanda yanzu akwai kashi 36 cikin 100 na matan da ke yin jinin al'ada su miliyan 336 da ke amfani da audugar,
Sauran 'yan matan na amfani da tsofaffin kaya ne wajen taƙaita zubar jinin, kuma kimanin 'yan mata miliyan 23 ana korarsu daga makaranta a ko wacce shekara ne saboda sun fara al'adarsu yayin da suke cikin makarantar.
Amma saboda matakan kulle da aka sanya sakamakon cutar korona da ta janyo kulle makarantu, shi ma shirin raba audugar ya tsaya cik.
"Na karɓi audgata ta ƙarshe ne a watan Fabrairu," in ji Priya. "tun daga nan, sai dai in saya a shagon sayar da magani. Sai na ba da kusan rupee 30 ake bani fakitin audugar mai dauke da guda bakwai ciki."
Priya na cikin yara masu sa'a tun da iyayenta za su iya ba ta kuɗi ta saya. Da yawa daga cikin makwabtansu sun rasa ayyukansu ko abinci ba sa iya saya. 'Yan matan da ke irin wadannan gidajen sai dai su yi amfani da tsofaffin kaya yayin da al'adar ta zo mu su.
Gaba kaɗan daga gidan su Priya da ke Badli akwai unguwar Bhalaswa Diary, inda wani gidan yawa yake, mai dauke da iyalai sama da 1,900.
Madhu Bala Rawat, wata mai fafutuka ce da ke zaune a unguwar, kuma a nan take aiki, ta nuna damuwa matuƙa game da ƙarancin audugar matan ga 'yan matan da ke zuwa makaranta:
"Jinin al'ada ba zai tsaya ba lokacin wannan annobar, ci gaba da zuba zai yi. Audugar na da muhimmanci a wajen mata, mai yasa gwamnati za ta wofuntar da bukatunmu?"

Asalin hoton, Getty Images
"Mafi yawan 'yan matan da ke wannan yankin, ciki har da 'yata mai shekara 14, sun dogara ne kan audugar da makarantu ke basu, saboda ba za su iya siya ba," in ji ta.
"Yan matan na cikin damuwa, yaya za su yi da al'adarsu yanzu? Ba sa son yin amfani da tsumma ko kadan. kamata ya yi gwamnati ta rika samar da wannan audugar a wata-wata."
Daga baya Misis Rawat ta aike da sakon taimako zuwa wata kungiya da ke aiki kan tsaftar jinin al'ada da ake kira Womenite, ta raba fakitin audugar 150 a yankunan Badli da kuma Bhalaswa Diary a watan Afirilu.
Harish Gupta shi ne shugaban kungiyar Womenite, ya ce suna kara neman taimakon kudi da za su raba auduga 100,000 nan gaba a Delhi, da kuma wasu yankunan da ke zagaye da birnin, nan da watan Mayu, wanda zai yi daidai da ranar tsaftar jinin al'ada ta duniya da ake bikinta duk ranar 28 ga watan.
"Za mu fara rabon nan da 'yan kwanaki masu zuwa," ya shaida wa BBC.
Akwai irin waddan kungiyoyin a faɗin Indiya da dama.
Wani kamfani hada audugar a baya, ya raba auduga 80,000 a Delhi da Punjabi.
An dinga raba wannan auduga ta hannun jami'an tsaro a birane irinsu Bangalore, Hyderabad da Jaipur da Chandigarh da Bhubaneshwar da kuma Kolkata, su suke zuwa gida-gida suna rabon a unguwannin marasa gata da kuma sansanin 'yan ci-rani.

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin, jami'iyya mai mulki ta Bharatiya Janata Party (BJP) ta sanar da shirinta na raba wa 'yan mata da manyan mata fakitin auduga 600,000 ta hannun jami'an 'yan sanda a yankunan masu cunkoso na Delhi.
Ba kawai a birane matsalar ta tsaya ba, karancin audugar ya game duka fadin kasar, amma matsalar ta fi ƙamari a kauyuka, in ji Shailja Meta, wata mai aiki da wata ƙungiyar da ke taimakon masu rauni.
"Yayin tattaunwarmu da abokan hulɗarmu a wasu jihohin, sun shaida mana cewa kashi 15 ne cikin 100 ne kawai ke iya samun audugar a lokacin kulle.
"Bayan rufe makarantu, 'yan matan kawai na samun audugar ne ta a hannun masu aikin lafiya wadanda ke raba 'yar kaɗan da suke da ita."
Wannan matsalar ta samo asali ne lokacin da Indiya ta ƙaƙaba dokar kulle a fadin ƙasar ranar 25 ga watan Maris, kuma ba a sanya audugar mata ba cikin abubuwan da ke da muhimmanci wanda dokar ta ɗagawa kafa.
A ranar 29 ga watan Maris ne kawai, bayan wani kantin sayar da magani da wani shafin intanet suka yi korafin audugarsu ta kare, shi ne ya sa gwamnati ta sanya audugar cikin kayayyaki masu mahimmanci a kasar.
Wannan jinkirin ya haifar da asarar samar da audugar na kusan kwana 10.
"Bayan gwamnati ta yarda kamfanin ya ci gaba da aiki, ya dauke mu kwanaki uku zuwa hudu mu sake farfaɗo da kayan kamfani da muke buƙata don bai wa ma'aikatanmu," in ji Rajesh Shah, wanda shi ne shugaban kungiyar Feminine and Infant Hygiene.
Mista Shah ya ce ana aikin samar da audugar ne sama-sama saboda matsalar ƙarancin ma'aikata wadanda suka bar birane suka koma ƙauyukansu saboda dokar kulle.
"Kashi 60 cikin dari ne na kamfanin ke aiki, amma babu wani kamfani da ke aiki kamar yadda ya keyi a baya. Akwai karancin ma'aikata, ma'aikatun da ke shiyyoyin da aka kafa dokar ba a barsu sun dawo aiki ba, akwai kuma wagegem gibi wajen samar da audugar."
Akwai matukar ƙarancin audugar, in ji Mista Shah, yana kuma jan kunnen yanayi ka iya munana kafin a shawo kan matsalar.

Asalin hoton, Getty Images
Tuni aka fara ganin tasirin matsalar a lungu da sakon Indiya.
Tanya Mahjan ta kungiyar Menstrual Health Alliance of India (MHAI), wata gamayyar kungiyoyin masu zaman kansu, masu samar da audugar da kuma masana masu wayar da kai kan al'adar mata, sun ce abokan huldarsu a fadin kasar na kukan wagegen gibin da ake fuskanta wajen samar da audugar musamman a yankunan birane.
"Bayan wuya sai daɗi" in ji ta.
"A kauyuka, inda babu audugar a dakunan ajiye kaya, mutane na tafiya garuruwan kusa ko kuma yankunan da ake da nisan kilomita 10 zuwa 40. Kamar yanzu kuma da aka sanya dokar takaita zirga zirga, da dokar ba da tazara ana fuskantar karancin abubuwan hawa."
Da yawa 'yan mata ba za sa iya tambayar mazan gidansu ba, cewa su saya musu auduga, saboda tambayar tamkar rashin kunya ce.
Sakamakon haka, Misis Mahajan ta ce, mafi yawan 'yan matan da suka dogara kan samun audugar daga makarantunsu yanzu na amfani da tsofaffin kaya ne a madadin ta.
La'akari da cewa Indiya na amfani da biliyoyin auduga a duk fadin Indiya, masu wayar da kai na ba da shawarar amfani da kayan da basu tsufa ba don za su fi zaman zabi mai kyau.
Ba tare da la'akari da wane irin tufafi aka yi amfani ba, tsaftar ita ce abin da ya fi muhimmanci, kayan da za a yi amfani da su kasance na auguda, a kuma wanke su yadda ya kamata a shanya su su bushe cikin rana kan a sake amfani da su, in ji Arundati Muralidharan na kungiyar ba da agaji ta WaterAid.
Za kaji kamar da sauki, to amma ba abu ba ne mai saukin cimmawa ba.
A yankin da ke da cunkoso, lokacin da kusan dukan mazaje ke gida saboda dokar kulle, 'yan mata da manyan mata a kauyuka na shan wahala wajen amfani da bandaki akai-akai kamar yadda suka saba, samun karin ruwan da za su wanke augudar da kuma wurin da za su shanya su cikin rana da za su bushe ba tare da wata wahala ba.
"Da yawa daga cikin abokan huldarmu sun shaida mana cewa lafiyar mata a wannan lokaci na annobar korona ya fada cikin damuwa, kuma ya kamata a magance wannan matsala," in ji Misis Muralidharan.











