Lafiya Zinariya: Shin haihuwa na janyo tabin hankali?

Bayanan sautiLafiya Zinariya kan matsalar kwakwalwa bayan haihuwa

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar:

Bayan radadin nakuda da mata kan fuskanta a yayin haihuwa, wasu matan kan hadu da wani ciwo da kan shafi rayuwarsu bayan haihuwa.

Wasu masana sun bayyana cewa tsananin damuwa da wasu matan kan fada ciki kan shafi tunaninsu ta yadda a wasu lokutan za su dinga yin wasu abubuwa kamar wadanda suka zautu.

Akasari a kasar Hausa rashin fahimtar wannan yanayi yasa a kan yi tsammani mace ta hadu da aljanu.

Wannan cuta ta tsananin damuwa kan sa wasu matan su raunata jariransu ko ma su yi yunkurin kashe su ko su kashe kansu.

Matsala ce wadda ba ta tsaya kan mata na nahiyar Afrika kadai ba har ma da wasu kasashen da suka ci gaba na duniya.

Ga wasu shirye-shiryen na baya da za ku iya karantawa