Lafiya Zinariya: Illar rashin tsafta ga mata

Mata

Asalin hoton, Getty Images

Masu iya magana dai kan ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya! To albishinku, a yau uwar diyar ma ba zata ji kunyar ba domin sashen Hausa na BBC ya shirya tsaf don fara gabatar muku da wani sabon shiri, 'Lafiya Zinariya.'

Lafiya Zinariya shiri ne da zai duba batutuwan da suka shafi kiwon lafiyar mata da suka hada da cucuttuka, hanyoyin kauce musu da matakan neman magani tun da wurwuri.

Kazalika, a wannan sabon shiri wanda zai rika zuwa muku a duk mako, za mu tattauna da kwararrun likitoci da sauran masana a fannin kiwon lafiya da majinyata, don jin yadda rayuwa ta kasance musu, har ma da masu jinyar a wasu lokutan.

A yau cikin shirin za mu duba batun da ya shafi tsaftar jikin mace.

Wani batu da ke ci wa mata tuwo a kwarya musamma a Arewacin Najeriya shi ne yadda za a gyara jiki.

A mafiya yawan lokuta akan samu yanayin da aure ke mutuwa sakamakon gyara tsaftar jiki.

To sai dai bincike ya nuna cewa mata da dama na son ganin su tsaf-tsaf amma kangin talauci da suke ciki ya sa sai dai su gani a makwabta.

Wannan layi ne

Hakazalika, ana ganin wasu matan mazansu ne ba su damu da su sayo masu kayan gyaran jiki ba, duk da cewa maza na matukar kaunar macen da take da tsaftar jiki.

Ku latsa wannan alamar lasifikar da ke kasa domin jin yadda shirin ya kasance.

Bayanan sautiHabiba Adamu