Za mu daga likkafar Dambe a duniya - Sunday Dare

Sunday Dare
Bayanan hoto, Ministan wasannin Najeriya da wasu matasan 'yan dambe

Najeriya ta ce za ta shigar da Dambe cikin jerin wasannin kasar, kamar su kwallon kafa da na kwando da dai sauransu.

Ministan wasanni da matsa na kasar, Sunday Dare ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da BBC Hausa.

Sunday Dare ya ce gwamnatin kasar za ta shiga cikin wasan gadan-gadan domin tabbatar da cewa an habaka shi ya kuma karbu a ko'ina cikin kasar.

"Za mu ga yadda za mu kawata wasan da tsara masa dokoki na musamman, sannan mu dauke shi zuwa kasashen nahiyar Afrika da ma duniya baki daya."

Ministan ya ce cibiya za a gida ta yadda za a rinka horas da matasan da ke da sha'awar Damben domin ganin an anfana da baiwar da suke da ita.

"Ganin yadda Dambe ya zama wata hanyar samar da zaman lafiya tsakanin al'ummar Najeriya yasa dole gwamnati ta mai da hankali ciki."

Latsa wannan hoton na kasa domin kallo da sauraron Sunday Dare

Bayanan bidiyo, Sunday Dare
Wannan layi ne

Menene Dambe daga Buhari Muhammad Fagge

Wasu 'yan dambe yayin wasan
Bayanan hoto, Dambe dai wani wasan kokowa ne da ya samo asali daga Arewacin Najeriya da wasu sassan kasar Nijar

Dambe dai wani wasan kokowa ne da ya samo asali daga Arewacin Najeriya da wasu sassan kasar Nijar.

Kuma wasan ya kwashe shekaru ana gudanar da shi, sai dai a baya-bayan nan ya samu wata karbuwa ga matasan kudancin Najeriya da kuma masu bibiyar al'amuran yau da kullum.

A yau Damben yana neman tashi daga wasan 'yan Arewacin kasar, saboda tuni wasu kabilu da ke kudancin kasar su ma suka fara gudanar da wasan a yankunansu.

A baya dai ana sanya kyautuka irin su Shanu da kudade, amma a yau ana sa motoci da babura kai harma da gidaje.