Napoli ta kori Ancelotti duk da ya ci wasa a Champions League

Carlos Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ancelotti ya fara horas da Napoli a bara

Napoli ta kori kocinta Carlo Ancelotti kasa da sa'a uku bayan ya tsallakar da ita zagayen 'yan 16 a a gasar Champions League a daren jiya Talata.

Kubgiyar ta buga wasa tara ba tare da nasara ba har sai ranar Talatan da ta ci Genk 4-0 a gidanta.

Wannan ce kaka ta biyu da kocin ke rike da kungiyar, amma yana matsayi na bakwai a Serie A, saboda gaza katabus da ya yi.

Napoli ce kungiyar kadai ta ci Livrpool a kakar bana a minti na 90, inda ta cinye ta 2-0 a watan Satumba.

A watan jiya an samu wata babbar rashin jituwa tsakanin kocin da 'yan wasan Napoli da kuma shugaban kungiyar Aurelio de Laurentiis.

De Laurentiis ya bayar da umarnin a halarci wani atisaye amma Anceloti da 'yan wasan duka suka ki halarta suka koma gida.

Anceloti wanda ya lashe Premier Ingila da FA biyu a Chelsea a kakar 2009-2010, ya samu tayin karbar aikin horaswa a Arsenal da kuma Everton.

Yana daya daga cikin koci ukun da suka lashe Kofin Zakarun Turai mna Champions League uku tare da tsohon kocin Liverpool Bob Paisley da kuma Zinedine Zidane da ke rike da Real Madrid a yanzu.

Ancelotti ya lashe Champions League biyu a AC Milan sannan ya lashe daya a Real Madrid da kuma wasu kofunan cikin gida tare da AC Milan da Chelsea da Paris St-Germain da kuma Bayern Munich.

Carlos Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ancelotti ya lashe Champions League biyu a AC Milan, daya a Real Madrid da kuma wasu kofunan cikin gida tare da AC Milan da Chelsea da Paris St-Germain da Bayern Munich

Da alama bai san za'a sanar da korar tasa ba, bayan nasarar da ya samu kan Genk ya ce: "Zan tattauna da Shugaba De Laurentiis gobe domin mu dauki matakin da ya kamata kan Napoli.

"Nasarar da muka samu za ta kara mana kaimi kuma za ta kara karfafa wa 'yan wasan gwiwa a nan gaba."

Amma cikin dare sai ya ga sanarwar cewa: "Napoli ta yanke hukuncin raba gari da kocinta Carlos Anceloti."

Ta ci gaba da cewa: "Amma alaka da girmamawa tsakanin kungiyar da shugabanta Aurelio de Laurentiis da kuma Carlos Ancelotti na nan daram."

Rahotannin kafafen yada labaran Italiya na cewa Gennaro Gattuso, wanda AC Milan ta sallama a kakar da ta gabata na cikin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Ancelotti.