George Floyd: Tsofaffin shugabannin Afirka sun yi tur da kisan baƙar fata

Asalin hoton, Getty Images
Tsofaffin shugabannin kasashen Afirka sun yi tur da kisan da wani dan sanda ya yi wa wani bakar fata George Floyd a Amurka a yayin da ake ci gaba da zan-zangar kyamar kisan nasa a fadin kasar.
Kungiyar tsofaffin shugabannin kasashe da gwamnatocin Afirka ta bukaci shugabannin Afirka masu ci su "nuna matukar rashin amincewa" kan kisan sannan su nemi a hukunta "wadanda suke da alhakin kisan da ma wasu laifukan kafin wannan", a cewar sanarwar da tsohon shugaban kasar Benin Nicéphore Soglo ya fitar.
"Wannan irin ƙeta ce da ya kamata dukkan duniya ta yi tur da ita domin ta wukalanta dan adam. Wane ne ya isa ya fito ƙiri-ƙiri a nan ya wulaƙanta Turawa, ko Larabawa ko Indiyawa, ko 'yan ƙasar China, ko Japanawa, ko 'yan kasar Argentina, da makamantansu a nan. Wannan wulakanci ya isa haka," in ji shi.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addoya wallafa sakon Twitter inda ya yi Allah-wadai da kisan Floyd.
Ya ce: "Muna goyon bayan 'yan uwanmu da ke Amurka a wannan mawuyacin hali, kuma muna fatan wannan kisa da aka yi wa George Floyd zai kawo karshen wariyar launin fata da ake nunawa a Amurka."
Jam'iyyar African National Congress (ANC) da ke mulki a Afirka ta Kudu ta bukaci Shugaba Cyril Ramaphosa ya tattauna da hukumomin Amurka da zummar "kashe kaifin tayar da jijiyoyin wuya da ake yi game da wariyar launin fata tsakanin kabilu da al'uma daban-daban".

Asalin hoton, Getty Images







