Hotunan zanga-zangar adawa da kashe wani bakar fata a Amurka

A protesters stands by a fire near the White House in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

An yi tashe-tashen hankula a birnin Washington na Amurka har cikin dare, yayin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da kashe wani bakar fata da 'yan sanda suka yi a birnin Minnesota.

George Floyd mai shekara 46 ya mutu ne a hannun wani dan sanda farar fata da ya kwantar da shi a kokarin hana shi guduwa.

Protesters rally outside the White House in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, wasu dumbin masu zanga-zanga suka sake taruwa a gaban Fadar White House don nuna bacin ransu kan kisan
A protester kicks an object into a fire near the White House in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan karon sai da masu zanga-zangar suka kunna wuta suka kona shingaye
A protesters throws a stone at police (in the background) in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ga wasu na jifan 'yan sandan kwantar da tarzoma da aka baza a birnin da duwatsu da sauran abubuwa
Torched cars in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kona motoci tare da lalata abubuwa da kuma sata
Protesters burn a US flag in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi ta daga tutocin Amurka ana kona su
Police clash with protesters near St John's Church in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An sa wuta a kasan Majami'ar St John's Episcopal - wani gini mai dadadden tarihi da ke kusa da Fadar White House. Kowane shugaban kasar Amurka ya halarci cocin a kalla sau daya tun bayan gina ta a shekarar 1816.
People run as police disperse demonstrators in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun yi amfani da gurneti don tarwatsa taron mutanen
Police detain protesters in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daga baya 'yan sanda sun kama mutane da dama
Riot police secure the area around the White House in Washington DC. Photo: 31 May 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta kokarin shawo kan masu zanga-zangar don kare Fadar White House. Kazalika rahotanni sun ce a ranar Juma'a Shugaba Donald Trump ya buya a wani gini da ke karkashin kasa a fadar.

Dukkan horunan suna da hakkin mallaka