George Floyd: Trump ya yi barazanar aika sojoji su fatattaki masu zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Donald Trump ya yi barazanar aika sojoji domin su kwantar da tarzomar da ake fama da ita a Amurka kan mutuwar da wani bakar fata ya yi a hannun 'yan sanda.
Ya ce idan birane da jihohi suka gaza shawo kan zanga-zanga da kuma kare mutanensu zai aike da sojoji don su yi gaggawar shawo kan matsalar.
Ana ci ga da yin zanga-zanga kan kisan George Floyd, wanda ya mutu a makon da ya gabata.
An harbi 'yan sanda hudu tare da ji musu rauni a Missouri, sannan rahotanni sun ce an kashe mutum biyu a sanadin zanga-zangar a Chicago.
Shugaban 'yan sanda na St Louis da Missouri Kanal John Hayden Junior, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan sanda na tsaye ne a kusa da wani layi a yayin da ba zato ba tsammani suka ji wani zafi. Amma ba su ji karar harbin ba.
Ya ce: "Wasu bata gari sun harbi 'yan sanda kuma a yanzu haka hudu suna asibiti a kwance. Mun gode wa Allah suna nan da ransu kafin su dawo cikin hayyacinsu.
Sai dai babu karin bayani kan rahotannin kashe-kashen da aka yi a Chicago.
Kazalika, gomman birane sun sanya dokar hana fita a ranar Litinin da dare.
Birnin New York na cikin dokar kulle har zuwa karfe 9 na safe agogon GMT a ranar Talata, sannan birnin Washington DC ya tsawaita dokar hana fita na karin dare biyu.

Asalin hoton, Reuters
A New York, an balle wani babban kanti na Macy sannan an yi sace-sace a shagon Nike, yayin da aka fasa kofofi da tagogin wasu shagunan.
An kama mutane da dama. Dokar hana fita za ta fara aiki a birnin daga karfe 8 na dare agogon GMT.
An fara jerin zangar-zangar ne bayan da wani bidiyo ya bayyana da yake nuna yadda aka kama Mista Floyd, mai shekara 46, kuma wani dan sanda ya kwantar da shi a kasa tare da dora gwiwarsa a kan wuyan Floyd na tsawon lokaci, har yana ta rokon dan sandan da cewa ba ya iya numfashi.
Tuni dai aka fara tuhumar dan sanda Derek Chauvin da laifin kisan kai kuma zai bayyana a kotu a mako mai zuwa. An kuma kori wasu 'yan sandan uku daga aiki.
Kisan Floyd ya dawo da radadin kashe Amurkawa bakaken fata da aka dade ana yi da 'yan sanda ke yi da kuma nuna wariya. Wannan ya biyo bayan manyan kashe-kashe irin na Michael Brown da aka yi a Ferguson, da Eric Garner a New York da kuma wasu da dama da suka jawo aka kirkiri fafutukar 'Black Lives Matter movement' wato ran bakar fata na da muhimmanci.
Ga mutane da dama, rikicin na nuna yadda aka shafe shekaru ana jin takaici kan nuna wariya da rashin daidaito.
Me Trump ya ce?
Shugaban kasar ya yi wani gajeren jawabi daga wani Lambun Fure na Fadar White House Rose Garden, a yayin da ake iya jiyo hayaniyar masu zanga-zangar da ake kokarin tarwatsawa.
Mista Trump ya ce ''dukkan Amurkawa sun ji takaicin kisan gillar da aka yi wa George Floyd" ya kara da cewa ''amma bai kamata wasu bata gari su banzatar da tunawa da shi ta hanyar da ba ta dace ba.''
Ya bayyana irin sace-sace da rikicin da aka yi a birnin a ranar Lahadi a matsayin ''babban abin kunya'' kafin ya sha alwashin daukar matakan kare birnin.
''Zan aike dubban sojoji masu makamai, da jami'an tsaro don dakatar da zanga-zanga mai cike da rikici da sace-sace da lalata wurare da dukiyoyi,'' a cewar Trump.
Daga nan sai Mista Trump ya mayar da hankalinsa kan zanga-zangar da ake yi a fadin kasar, inda ya zargi ''kwararrun masu tayar da hargitsi'' da kuma wata kungiyar Antifa mai adawa da mulkin kama karya.
A ranar Lahadi ya ce yana da niyyar ayyana kungiyar Antifa a matsayin ta ta'addanci.
Ya yi kira kan birane da jihohi don aike sojojin ko-ta-kwana masu dumbin yawa don mamaye tituna.
Zuwa yanzu an aike da dakaru 16,000 daga rundunar don dakile tashin hankalin.
Mista Trump ya kara da cewa: "Idan wani birni ko wata jiha suka ki daukar matakan da suka dace... to zan aike da sojojin Amurka da kaina don su magance matsalar da gaggawa.''
''Ina son masu shirya wannan ta'addanci su san cewa za su fuskanci hukuncin manyan laifuka,'' in ji shi.
Sai dai kalamansa sun fuskanci suka nan da nan daga wani jigo a jam'iyyar adawa ta Democrats - Joe Biden - inda ya ce Mista Trump yana amfani da sojojin Amurka don su yaki Amurkawa.

Amfani da karfin soji?

An shafe ranar Litinin ana matsa wa Donald Trump lamba don magance rikicin da ake fama da shi a manyan birane a fadin Amurka.
A yayin da rana ke faduwa a Washington Dc, a wani jawabi na gaggawa da aka shirya yi a Fadar White House, shugaban kasar ya bayyana matakan da zai dauka.
An gargadi gwamnoni cewa idan ba su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi a kan tituna ba, to shugaban zai yi amfani da tsohuwar doka ta daruruwan shekaru ta hanyar aike sojoji a cikin Amurkan.
Tuni dai ya dauki matakin tura sojojin zuwa gundumar Columbia wadda ke karkashin ikon gwamnatin tarayyar kasar.
Kafin shugaban kasar ya yi jawabi, ya yi alkawarin yana bayan masu zanga-zangar, wadannan sojojin sun samu nasarar kawar da masu zanga-zangar daga Dandalin Lafayette Square, daga tsallaken titin Fadar White House.
Hakan dama ce da aka bude hanya inda shugaban kasar da manyan jami'ansa suka samu damar tattakawa zuwa Majami'ar St John's Church da ke kusa da fadarsa, wadda masu zanga-znagar suka dan lalata ta da wuta a wannan yammacin - ya dauki hoto a wajen da wasu za su yi masa kallon abin tarihi na musamman wasu kuma su kalle shi a matsayin abin da bai zama dole ba.
Ya tsaya a gaban ginin cocin da littafin baibul a hannunsa, ya yi alkawarin Amurka za ta dawo da karfinta nan ba da jimawa ba.
Sai dai bai tabo batun kawo sauye-sauye a bangaren 'yan sanda ko batun abin da ya jawo zanga-zangar ba a makon da ya gabata kwata-kawata a jawabin nasa.
A maimakon haka, ya ce shi ne shugaban kasa mai doka da oda - wata alama da ke nuna cewa matakin da zai dauka don kawo karshen rikicin na amfani da karfin soji ne.

Me ya faru a baya-bayan nan kan zanga-zangar?

Asalin hoton, AFP
An yi zanga-zanga a fiye da birni 75 kan abin da ya faru da George Floyd. Tutunan da a kwanaki kadan da suka wuce suka zama tamkar kufai saboda annobar cutar korona sun cika makil da masu zanga-zanga da ke tafiya kafada da kafada.
A ranar Litinin da yamma kuma aka kara yin zanga-zanga kuma birni kusan 40 sun tsawaita dokar hana fita.
Dubban mutane sun yi maci a New York, lokaci kankani kafin dokar hana fitar ta fara aiki. 'Yan sanda sun kama mutane da dama sannan an fasa shaguna a Manhattan.
An kuma yi wasu kananan zanga-zangar a birane kamar su Los Angeles da Oakland.
A Kentucky kuwa, an kori shugaban 'yan sandan Louisville ne daga aiki bayan da 'yan sanda suka yi harbi kan masu zanga-zangar a ranar Lahadi da dare, inda har wani mutum da ke harkokin kasuwancinsa a gefe ya rasa ransa.












