Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Tun daga ranar Lahadi, 17 ga watan Mayun 2020 zuwa ranar Asabar, abubuwa da dama muhimmai sun faru a Najeriya kuma sun ja hankulan 'yan kasar.

Mun tsakuro muku muhimmai daga cikinsu.

Najeriya ta kama jirgin Birtaniya da ke 'jigilar fasinjoji'

..

Asalin hoton, Getty Images

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar wa BBC da kama jirgin a wata tattaunawa inda ya ana gudanar da bincike kuma jirgin zai biya tara mai matukar yawa.

Ministan ya tabbatar da cewa jirgin yana jigilar mutane cikin Najeriya har zuwa jihohi kamar Abuja da Legas da kuma Oyo duk da annobar korona da ake ciki.

Ya bayyana cewa an bai wa jirgin dama gudanar da ayyukan jin ƙai, amma ya ɓige da jigilar fasinjoji.

Buhari ya bai wa sojoji umarnin kakkabe 'yan bindiga a Katsina

.

Asalin hoton, Buhari Sallau

A makon nan ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar umarnin gudanar da wani shiri na musamman domin fatattakar barayi da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina.

Shugaban ya bada izinin ne a yayin da jama'ar jihar da ma wasu jihohi na makwabtanta ke koka wa kan ci gaba da tabarbarewar tsaro, wadda aka yi imanin ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da raba dubbai da muhallansu cikin watannin baya-bayan nan kaɗai, duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa a halin yanzu dakaru na musamman na nan na aiki, sai dai a cewarsa ba za a fallasa irin abubuwan da suke yi ba.

Tuni dai dakaru na musamman suka isa jihar domin fara aiki, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana, sai dai a cewarsa ba za a fallasa irin abubuwan da suke yi ba.

Saudiyya ta mayar da 'yan Najeriya kusan 300 gida

.

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Laraba ne Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya wallafa wata sanarwa a shafinsa na Twitter inda ya ce sun karbi 'yan Najeriya mutum 292 da suka makale a Saudiyya.

Ministan ya ce jirgin Saudiyya ne ya kai mutanen filin jirgin sama da ke birnin Abuja a daren Talata inda ya ce mafi yawancin mutanen da aka mayar da su Najeriyar mata ne masu shayarwa da kananan yara.

Mista Onyeama ya bayyana cewa an killace mutanen a otal inda ake sa ran za su kai makonni biyu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanadar wajen gane ko suna dauke da cutar korona ko a a.

Wannan ce dai tawaga ta baya-bayan ta 'yan Najeriyar da suka makale a kasashen waje a zamanin korona.

Coronavirus: An tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyu

..

Asalin hoton, @DIGICOMMSNG

A ranar Litinin ne kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona ya sanar da cewa an tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyu biyo bayan ƙarewar wa'adin a ranar ta Litinin.

Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin ƙasar, shi ne ya sanar da hakan a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan daƙile cutar korona a Abuja.

Duk da sassaucin fita na kwana biyu da mutanen Kano ke da shi, haramcin taruka da suka haɗa da na addini na nan daram.

Kazalika su ma matakan nesa-nesa da juna da aka ɗauka da suka haɗa da zirga-zirga tsakanin jihohi an tsawaita su da mako biyu.

Kotu ta yanke wa Yunusa Yellow hukuncin daurin shekara 26

..

Asalin hoton, YUNUSA YELLOW

A wannan makon ne wata babbar kotu da ke zama a birnin Yenagoa da ke jihar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Ɗahiru da aka fi sani da Yunusa Yellow daurin zaman gidan kaso na shekara 26 bisa samun shi da laifin safara da cin zarafin Ese Oruru.

A shekarar 2015 ne dai mahaifan Ese Oruru suka yi zargin Yunusa Yellow da yin 'garkuwa' da 'yarsu, ya kuma kai ta jihar Kano inda ya tilasta mata aurensa har ma aka samu juna biyu.

Wannan batun dai ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin 'yan kudu da arewacin Najeriya, musamman bayan da ta bayyana cewa Ese Oruru ta musulunta inda ta bar addininta na Kirista.

Alkalin kotun dai ya ce ba a samu Yunusa Yellow da laifin na farko ba na garkuwa da mutum, to sai dai ya ce an same shi da laifin safarar kananan yara da yin jima'i ba tare da amincewa ba da cin zarafi.