Coronavirus: Sharudan yin sallar Juma'a da Idi a Kano

FACEBOOK/SALIHU TANKO YAKASA

Asalin hoton, FACEBOOK/SALIHU TANKO YAKASA

Bayanan hoto, Za mu bi matakan kariya yayin gudanar da sallolin

Gwamnatin jihar Kano ta gindaya wasu sharuddan da za a bi domin gudanar da sallolin Juma'a da Idi da ta amince za a yi a jihar a jiya Litinin.

Kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata tattauanwa da ya yi da BBC.

Malam Muhammad Garba ya ce ba a tabbatar da wannan umarni ba sai da aka naɗa wani kwamiti wanda zai tabbatar da an bi ƙa'idojin da aka shimfiɗa a kowanne masallaci.

Kwamitin wanda ya hadar da kwamishinan lafiya na jihar da na muhalli da wasu malamai da likitoci zai tabbatar babu wani masallaci da ya tsallake wadannan dokoki.

Cikin sharudan kuwa akwai samar da ruwa da sabulun wanke hannu da kuma sinadarin wanke hannu da ake kira Sanitizer a kowanne masallaci.

Kwamitin kuma zai tabbatar da cewa duk wanda zai shiga kowanne masallaci zai sa takunkumi domin kauce wa yaduwar cutar korona.

Da yake bayani kan sallar Idi kwamishina Muhammad Garba ya ce dukkan masallatan Idi da ke fadin jihar Kano za a gudanar da sallar, domin rage cunkoso da tabbatar da dokar ba da tazara.

Karin bayani kan coronavirus

Sai dai da alamun har yanzu kwamitin bai gama tsara yadda za a gudanar da wadannan salloli ba, amma ya ce zai nemi hadin kan sauran hukumomin tsaron jihar don tabbatar da bin dokokin da aka shimfida.

Muhammad Garba ya bayyana cewa za a gudanar da karamar sallar ce lami ba tare da shagulgula ba, babu ko wanne hawa cikin hawan sallah da sarakuna ke yi na al'ada.

Tun da farko Muhammad Garba ya ce "An dauki matakan ne bayan shawarwarin da malamai suka bayar na ganin an shafe makonni hudu ba tare da gudanar da sallar Juma'a ba a wannan wata na Azumi".

Sai dai wannan watakin da alama bai yi wa gwamnatin tarayyar Najeriyan daɗi ba, domin ko ta nuna rashin jin dadinta na sabani da ake samu game da matakan da take dauka da kuma wanda jihohi ke dauka akasinsu.

A ranar Litinin ne Gwamnatin tarayyar ta ba da umarnin tsawaita dokar kulle ta mako biyu a jihar ta Kano a wani mataki na yaki da annobar korona.

Wanda hakan ya kai makonnin da ta sanya zuwa hudu a jere bayan karewar wa'adin mako biyu da ta kakaba tun da fari.