Coronavirus: Ko Buhari da Ganduje sun raba gari ne?
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge
Mu kwana lafiya
Mun zo karshen labarai da rahotannin da muke ba ku a wannan
bangare na wannan rana. Sai
ku tara gobe domin samun sabbin labarai da rahotanni. Amma za ku iya lekawa kasa don karanta labaran da muka
wallafa.
Kafin sannan, ga kanun wasu daga cikinsu:
·Mai cutar korona ta
haifi 'yan biyu a Legas
·Matsalar tsaro Arewa
'ta fi karfin jami'an tsaron Najeriya'
·'Kananan yara ba za su iya yaɗa korona ba kamar manya'
·Portugal ta sake
buɗe wuraren shan shayi da makarantu
·Sudan ta tsawaita
dokar kulle gabanin bikin sallar Idi
Kada ku manta za ku iya bibiyarmu a
shafukan sada zumunta inda za ku tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.
Mu kwana lafiya.
Coronavirus: Ko Buhari da Ganduje sun raba gari ne?
Asalin hoton, Presidency
Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin gamsuwarta da yadda ake samun sabani tsakanin matakan da take dauka kan yaki da korona da kuma matakan da wasu jihohi ke dauka a nasu bangaren.
Wannan na zuwa ne bayan tsawaita dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin ta yi a Jihar Kano da mako biyu gaba.
A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da wasu gwamnonn jihohi ta Intanet kan batun yaki da cutar korona da kuma batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro.
Sai dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi hadin kan jihohin, inda ya ce gwamnatin Tarayya na tufka wasu jihohin na warwarewa.
A tattaunawarsa da BBC Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaban kan harakokin watsa labarai ya shaidawa cewa abin takaici ne a ce gwamnati tana daukan matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai.
A jiya Litinin ne dai Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya amince da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma'a da kuma Idi.
A wata sanarwa da Salihu Tanko Yakasai, mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan ya tattauna da wakilan Malamai 30 da kuma wasu jami'an gwamnatinsa ranar Litinin.
Sai dai ya ce ba za a bari mutane su yi shagulgula ba lokacin Sallar Idi. yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da dokar kulle.
Gwamnatin jihar ta bi sahun wasu jihohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma'a da na Idi.
Macron ya rasa rinjaye a majalisar Faransa
Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar shugaban Faransa Emmanuel Macron ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokoki bayan wata kungiyar 'yan majalisar ta balle daga jam'iyyar ta kafa sabuwar jam'iyya.
'Yan majalisar bakwai daga jam'iyyar La République en Marche za su mayar da hankali kan batutuwa kamar su Muhalli, Dimkoradiyya, da makamantansu.
'Yan majalisar da suka balle sun ce suna so su tabbatar da alkinta muhalli da daidaito tsakanin al'umma.
Ballewar tasu ta sa yanzu jam'iyyar Mr Macron tana da kujera 288 a majalisar, wato kasa da kujera daya domin yin rinjaye cikin majalisa mai mutum 577.
Masu sharhi a Faransa sun ce har yanzu La République en Marche (LREM) tana da goyon bayan jam'iyyu biyu, MoDem da kuma Agir, wadanda suke da kujeru 56 a Majalisar Dokokin.
Mece ce garkuwar jiki ta gama-gari?
A yayin da duniya ke ta kokarin ta samar da riga-kafin cutar Covid-19, mai yiyuwa mun ji ana cewa garkuwar jiki ta game gari?
Wannan wata hanya ce ta kare masu rauni a cikin al'umma domin yaki da cutar.
Masana sun ce ana samunta ne ta hanyoyi guda biyu.
Kalli bayanin dan jarida mai sa ido a kan coronavirus Abdulbaki Jari, domin sanin hanyoyin.
Bayanan bidiyo, Coronavirus: Mece ce garkuwar jiki ta gama gari?
Ban Ki-moon ya yaba da naɗa Gambari shugaban ma’aikatan Buhari
Sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya aike wa manema labarai ranar Talata ta ambato Mr Moon yana bayyana hakan a wasikar da ya aike wa Farfesa Gambari.
''Ina matukar taya ka murna a kan nadin da aka yi maka kwanakin baya a matsayin shugaban ma'aikatan Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya. Nadin naka wata nasara ce ba kawai ga shugaban Najeriya ba,har ma ga Najeriya da Afirka.
''Ina da kwarin gwiwa cewa kwarewar da ka yi lokacin da ka yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya, inda ka rike mukamai da dama, za ta taimaka maka wajen fuskantar kalubalen da cutar COVID-19 ta bijiro da su", in ji Ban Ki Moon.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ban Ki Moon da Gambari sun yi taba yin aiki tare a majalisar dinkin duniya
Cutar korona ta kashe mutum sama da 35, 000 a Birtaniya
Alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa kawo yanzu mutum 35,341 ne suka mutu sanadin cutar korona a Birtaniya.
Alkaluman, wadanda hukumar lafiya da walwalar jama'a ta kasar ta fitar ranar Talata, sun ce mutum 248, 818 ne suka kamu da cutar a fadin kasar.
Birtaniya tana cikin kasashen da annobar korona ta fi yi wa illa a nahiyar Turai.
Covid-19: CBN da NNPC za su ciyar da mutanen da aka killace
Asalin hoton, BBC Pidgin
Babban Bankin Najeriya -CBN ya
hada gwiwa da Kamfanin man kasar - NNPC wajen ba da gudummuwar naira biliyon daya don
dawainiyar kebe `yan Najeriya mazauna kasashen waje da ke komawa kasar.
Za a yi
amfani da kudin ne wajen ciyarwa da biyan kudin otal din da za a sauke sun a
tsawon kwana 14 domin tantance lafiyarsu, sakamakon yakin da ake yi da cutar
korona.
Tun da farko gwamnati ta dora alhakin wannan dawainiyar a kan masu
komawa kasar, lamarin da ya sa wasu suka yi ta kokawa.
Ma`aikatar harkokin wajen
Najeriya ce ta sanar da daukin da babban bankin kasar da kuma kamfanin man
Najeriyar suka kai na tallafawa da naira biliyon daya don rage dawainiya
ga `yan Najeriya mazauna kasashen ketare yayin da suka koma gida.
Ministan harkokin wajen
Najeriya, Geofery Onyema ne ya sanar da gudummuwar, wadda ya ce ma`aikatarsa ce
ta nemi taimakon, bayan ta fahimci cewa ba ta da sukunin ci gaba da biyan kudin
ciyarwa da na masaukin masu komawa kasar, wadanda yawansu ya zarta mutum 3,000.
Gwamnatin Syria za ta sanya ƙafar wando guda da hamshakin dan kasuwa
Gwamnatin Syria ta ƙara damarar sa ƙafar wando guda da hamshakin dan kasuwan nan Rami Makhlouf wanda tsohon na hannun damar shugaba Bashar Al-Assad ne.
Wani kundi dauke da sa hannun ministan kudin Syria da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna cewa an kwace kadarorin Mr Makhlouf da na matarsa har ma da na ya'yansa.
Takardun sun kira matakin a matsayin wata jingina don ganin cewa ya biya kudin da hukumomin sadarwar kasar ke bin shi.
Rami Makhlouf ya bayyanawa duniya cewa an tursasa shi da ya yi murabus daga shugabancin kamfanin Syriatel wanda mallakarsa ne
Mai cutar korona ta haifi 'yan biyu a Legas
Wasu likitoci a asibitin Jami'ar Lagos da ke Najeriya sun yi wa wata ma dauke da cutar korona tiyata inda suka ciro 'yan biyu.
A sakon da hukumomin asibitin suka wallafa a shafin asibitin na Twitter ranar Talata, sun ce jariran da aka ciro mace da namiji ne.
"Asibitin LUTH ya yi wa mai dauke da cutar korona ta hudu tiyata inda aka ciro jarirai biyu ( namiji mai nauyin 3.2kg da mace mai nauyin 3.25kg) ta hanyar tiyata.
“An ciro jariran ta hanyar tiyata ranar Talata, 19 ga watan Mayu. Mahafiyarsu da jariran suna cikin koshin lafiya; kuma kamar kowanne lokaci muna taya jajirtattun ma'aikantu murnar wannan gagarumin aiki da suka yi," a cewar sakon.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Matsalar tsaro Arewa 'ta fi karfin jami'an tsaron Najeriya'
Asalin hoton, @HQNIGERIANARMY
Bayanan hoto, 'An kashe fiye da mutum 8,000 a arewa maso yammacin Najeriya cikin shekara 10'
Kwararran masanin nan kuma mai sharihi kan al'amuran tsaro Group captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya, ya ce matsalar tsaron da ake fuskanta a Najeriya ta fi karfin jami'an tsaron kasar.
Group captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya, ya bayyana hakan a wata tattauanawa da ya yi da BBC, yana mai cewa "idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai".
Yana cewa duka ko ta ina Najeriya ba ta da cikakken shirin da za ta fuskanci wadannan matsalolin a yanzu.
"Ko an ci gabala kan wadannan mutanen ta wani dan lokaci ce saboda suna dawowa bayan lokacin kadan," in ji Group captain Sadiq.
"Babu isassun kayan aiki da sojojin Najeriya za su yi amfani da su don isa inda waɗannan mutanen suke, haka kuma da zukan da suke maƙalewa ciki sojojin ba za su iya shiga ba"
Da aka tambaye shi game da furucin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na bai wa hafsoshin sojin kayan aiki sai Group Captain Sadiq ya ce " na ji dadin furucin shugaban amma wannan ba abu ba ne na kusa ganin cewa kayan ba a nan ake samar da su ba".
Anan Group Captain Sadiq ya ce "Idan shugaba na magana a irin wannan lokaci da mutum biyu yake magana, na farko wadanda ya bai wa aiki cewa su kara kaimi, sai kuma wadanda hare-haren ke rutsa wa da su cewa su kara hakuri gwamnati na iya ƙoƙarinta wajen wannan yaƙi".
"Akwai tarnaki wajen cewa gwamnatin Najeriya take da shi na maganar tsaro, ba zai zama laifi ba idan ana ce mata babu abin da ta yi sai ta kara himma a nan gaba".
Wannan na zuwa ne dai dai lokacin da Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da 8,000, kana an raba wasu fiye da 200,000 da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekaru kimanin goma.
'Kananan yara ba za su iya yaɗa korona ba kamar manya'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Babu barazana ga ƙananan yara kan cutar korona
Biyu daga cikin manyan masana kimiyya a Birtaniya sun ce akwai alamun cewa kananan yara ba za su iya yada cutar Korona ba kamar yadda manya kan iya yadata.
Wannan na zuwa yayin da kasar ke mahawara kan sake bude makarantu bayan rufe su a baya da nufin dakile cutar Korona.
Dr Rosalind Eggo wanda mamba ne a kwamitin masana kimiyya da ke bai wa gwamnati shawara kan cutuka, ya shaida wa majalisar wakilai cewa yara ba su cika yada cutuka ba, duk da babu tabbacin haka dari bisa dari.
Shi ma wani mashawarcin gwamnatin John Edmunds ya ce kananan yara basu cika yaɗa cutuka ba, kuma a tarihi sau daya aka tabbatar da cuta ta yaɗu a wata makarantar Burtaniya.
Portugal ta sake buɗe wuraren shan shayi da makarantu
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani shagon shayi a birnin Lisbon
Portugal ta sake buɗe wuraren shan shayi da
cin abinci da kuma wasu shagunan, a wani sabon mataki na sassauta dokar kulle.
An sake buɗe wuraren rainon yara, tare da umartar yaran da su riƙa cire
takalmansu a bakin kofa da kuma takaita yawan yara a cikin ko wanne ɗaki.
Sai dai makarantu da dama sun ba da rahoton yara da yawa ba su koma ba, an kuma ba da dama ga iyayen da ba su gamsu da komawa makarantar ba da su zauna da
yaransu a gida.
Cutar korona ba ta yi ƙamari ba a Portugal kamar yadda ta yi a makobciyarta
Spaniya.
An hasko Firaministan kasar Antonio Costa a talabijin yana ziyartar wasu
shaguna a birnin Lisbon a karshen mako, kuma yana shawartar mutane su fito, su
ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Uganda za ta raba wa ‘yan kasarta takunkumi kyauta
Asalin hoton, AFP
Shugaban kasar
Uganda Yoweri Museveni ya ce gwamnatinsa za ta raba takunkumi kyauta ga dukkan ‘yan
ƙasar da suka haura shekara shida, kafin janye dokar hana zirga-zirga da aka
ƙaƙana saboda korona.
A farkon watan Mayu ne aka tilasta sanya takunkumi a cikin jama’a.
A wani bayani da ya yi a gidan talabijin na ƙasar a ranar Litinin, Mista
Museveni ya ce za a yi rabon takunkumin ne cikin kwana 14. Za a ba da takunkumi
daya ga ko wanne mutum.
Daga nan kuma za a ba da damar buɗe shaguna, masu motocin haya ma za
su ci gaba da ayyukansu.
Haka kuma haramcin motocin haya a kan iyakoki na nan daram har zuwa kwana 21 nan
gaba.
Za a bude makarantu amma ga yaran da ke shekarar karatunsu ta ƙarshe, domin rubuta jarrabawa.
Kasar dai ta kasance cikin dokar kulle na tsawon kwana 48.
Akwai mutum 260 da aka tabbatar suna dauke da cutar korona a kasar ya
zuwa yanzu, kuma yawancin su wadanda suka shiga kasar ne ta kan iyakar tudu ta
cikin manyan motoci.
Sudan ta tsawaita dokar kulle gabanin bikin sallar Idi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yanzu mako uku kenan ana fama da dokar kulle a Khartoom
Sudan ta ƙara
tsawaita dokar kulle a Khartoom babban birnin kasar da ƙarin mako biyu domin
taƙaita yaduwar cutar korona.
Kwamitin karta kwana na lafiya a kasar ne ya ba da wannan shawara, lokacin
da ake tunkarar shagulgulan sallar Eid Fitr a karshen watan Ramadana.
Kwamitin ya nuna fargabar taron mutane da za a samu yayin bikin salla wanda
zai iya haifar da ƙaruwar cutar idan an janye dokar, kamar yadda gidan raddiyon
Dabanga ya ruwaito.
Mataimakin shugaban kwamitin Siddig Tawir ya ce za a fitar da jerin dokoki
game da dokar anan gaba.
A watan jiya ne Firaiminista Abdalla Hamdok ya kori gwamnan jihar Khartoom bayan
ya nuna adawa da haramcin tarukan addini da aka ƙaƙaba domin shawo kan cutar
korona.
Akwai mutane 2,591 da ke fama da cutar a Sudan kuma mutum 105 tuni sun
mutu.
Babu wanda zai shigo Kaduna daga Kano - El-Rufa'i
Asalin hoton, Twitter
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa'i ya ce zai tabbatar babu mutumin da zai shiga Kaduna ranar Sallah kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma'a.
Yayin wani jawabi ga 'yan jihar tasa da yammacin Talata, Gwamna Elrufa'i ya ce "ni da kaina zan je hanyar shigo wa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. Cuta ta riga ta yi katutu a tsakanin mutane mu kuma mu bari su shigo mana da ita. Ba zai yiwu ba."
Har wa yau, gwamnan ya zargi jami'an tsaro da 'cin amana' inda ya ce jami'an tsaro na karbar na goro domin barin jama'a su shiga Kaduna.
Sabanin wasu jihohi, Gwamna Elrufa'i ya ce kowa ya yi sallar idi da Juma'a a gida domin hana bazuwar cutar korona da ke yi wa duniya barazana.
Gwamna Elrufa'i dai bai fadi lokacin da ake sa ran bude jihar ba, inda mataimakiyarsa ta ce har yanzu ba su gamsu da yanayin da cutar take a jihar ba ballantana su bude jihar.
Daga karshe Malam Nasir El-Rufa'i ya yi wa malamai Allah-ya-isa inda ya ce "ko a Makka ba za a sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau munbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa.
Isra'ila na ci gaba da sassauta dokar kulle
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Zafi na kara tsanani a kwanakin nan a kasar ta Isra'ila
Ministan Lafiya na Isra’ila ya janye dokar
da ta bukaci ‘yan makaranta su riƙa sanya takunkumi a cikin makaranta har zuwa ƙarshen mako, saboda matsanancin zafi da ake fama da shi.
Wannan matakin na zuwa ne daidai lokacin da
ƙasar ke ƙara sassauta matakan da ta ɗauka na hana yaɗuwar cutar korona – daga
gobe motocin haya za su ci gaba da aiki ba tare da ƙayyade adadin fasinjojin da
za su dauka ba.
Daga kuma ranar Larabar makon gobe, za a
buɗe wuraren cin abinci da gidajen rawa da wuraren shan barasa.
Ana dai ɗage wannan doka dubban ‘yan Isra’ila
suka yi cincirindo a gaɓar teku domin kaucewa zafi.
Firaiministan Losotho ya yi murabus saboda zargin kisan kai
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Duka ma'auratan ana tuhumarsu da hannu cikin kisan
Firaiministan
Lesotho ya sanar da yin murabus a hukumance biyo bayan zargin hannu da yake da
shi cikin kisan gillar da aka yi wa matarsa.
Thomas Thabane ya shaida wa gidan talabijin na kasar cewa duk da wa’adin
kammala aikinsa bai cika ba, zai yi murabus daga abin da ya kira babban matakin
barazana.
Ya kwashe watanni ana fama da shi ya sauka daga mukaminsa yana ƙi
Mista Thabane sun yi rabuwar baran-baran da matarsa Lipolelo, kuma an harbe
ta ne a kofar gidanta.
Ita ma matarsa ta yanzu Maesaiah ana tuhumar ta da hannu cikin kisan Lipolelo.
Duka ma’auratan sun musanta zargin aikata wani laifi.
Cutar korona ta soma ja baya a Indiya
Adadin masu dauke da korona a Indiya ya haura mutum dubu 100, kuma adadin sabbin masu kamuwa da cutar na nuna annobar na ja baya a kasar.
Duk da dokar kullen da aka yi fama da ita ta kimanin wata 2, an ta samun adadin sabbin masu dauke da cutar dubu 4 a kullum cikin makon da ya gabata.
Kimanin mutum 3,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar a fadin Indiya. Manyan birane kamar Mumbai da Delli da Channai na cikin inda cutar ta fi Kamari.
An tsawaita dokar kulle a kasar har sai karshen watan Mayu, duk da cewa wasu gwamnatin jihohin na ba da damar sake bude harkokin kasuwanci a inda suke.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan ne karo na hudu da ake tsawaita dokar fita a Indiya
Qatar ta musanta bullar korona a Doha
Asalin hoton, Getty Images
Qatar ta tabbatar da samun mutum 12 masu dauke da cutar korona a babban gidan yarin kasar, bayan wata kungiyar kare hakkin dan adam ta yi gargadin za a iya samun bazuwar annobar tsakanin mazauna gidan yarin.
Kungiyar Human Right Watch ta nemi hukumomin kasar ta Qatar da su samar da kyawawan matakan kariya ga mazauna gidan da kuma jami’an tsaron gidan yarin na Doha.
Kungiyar ta ce ta tattauna da wasu ‘yan kasar a gidajen yari shida da ake tsare da su, kuma sun bayyana mata mummunan halin da gidan ke ciki.
Qatar ta musanta bazuwar annobar tana mai cewa tuni aka garzaya da wadanda suka kamu da cutar zuwa wani asibitin kwararru.
'Yan sanda a Myanmar sun yi babban kamu
Asalin hoton, Reuters
'Yan sandan Myanmar sun kwace wata kwaya mai tarin yawa wadda yawanta ya sa rundunar ta ayyana ta da waddaa ba a taba gani ba.
An dai samu kwayar methamphetamine da kuma tabar wiwi ne a yankin jihar Shan da ke gabashin kasar.
Mutum 33 ne dai rundunar 'yan sandan ta kama masu alaka da kwayar a wani samame da ta gudanar a tsakanin watan Fabarairu da Afrilu.
Ana dai tsammanin kasar Myanmar ce kan gaba a kwayar methamphetamines a duniya.