Coronavirus: Boko Haram da Korona illarsu daya - Gwamna Zulum

Asalin hoton, @PROFZULUM
Gwamnan jihar Borno ya roki al'ummar Musulmin jihar da ka da su manta da addua'a Allah ya karya kungiyar Boko Haram da magoya bayanta.
Zulum ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da mai tamaka masa kan yada labarai Isa Gusau ya fitar.
Ya ce ''A kwana 10 na karshen watan ramadan mai alfarma, akwai yiwuwar musulman duniya za su mayar da hankalinsu ne kan yin addu'a a kan korana.
Ko shakka babu cutar annoba ce mai yi wa bil adama barazana.
Zulum ya ce ''Ina rokon Musulman Najeriya ka da su manta da irin barnar da Boko Haram ke yi.
Muna da annoba guda biyu a yanzu, wadanda matsayinsu daya kuma irin barnarsu daya."
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta Borno ta sake bude masallatai da majami'u a sakamakon gamsuwar da ta ce ta yi da yadda mazauna jihar ke bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar korona.
Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin yaki da Covid-19 a jihar Umar Usman Kadafur ne ya fitar da sanarwar, inda ya ce za a iya ci gaba da gudanar da ibadu a masallatai da majami'u amma da sharadin bayar da tazara da juna da kuma saka takunkumin rufe fuska.
Sai dai sanarwar gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da Sallar Idi ba saboda ba farilla ba ce, hakan na nufin ranar sallah mabiya addinin musulunci za su zauna a gida.


A sanarwar, gwamnatin jihar na nan kan bakanta na haramta sayar wa da kuma shan barasa da sauran kayan maye a jihar, inda gwamnatin ta sha alwashin hukunta wadanda suka karya doka.
Jihar Borno na cikin jihohin arewacin Najeriya da aka yi ta samun mace-macen mutane ba tare da sanin dalili ba, sai dai wasu masana na lakanta hakan da cutar korona.
Ya zuwa yanzu jihar Borno na da masu korona 188, mutum 20 kuma sun mutu haka kuma wasu 20 din sun warke da cutar.
Alkaluman ranar Laraba da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar sun nuna cewa mutum 184 sun sake kamuwa da cutar korona a fadin kasar. Yanzu adadin masu cutar 4, 971 a kasar.
Hukumar ta ce masu cutar fiye da 110 ne suka warke a ranar, abin da ya kawo yawan mutanen da suka warke daga annobar korona zuwa 1, 070, kuma 164 suka mutu.











