Coronavirus ta janyo cacar-baki tsakanin Ganduje da El-Rufai

El-rufai da Ganduje
Lokacin karatu: Minti 2

Da alama sakonnin da gwamnan jihar Kadunan Najeriya Malam Nasir El-Rufai, ya rinka wallafawa a shafinsa na Twitter a baya-bayan nan kan almajiran da aka mayar da su jihar daga Kano sun bata wa Ganduje rai.

A makon jiya Gwamna El-Rufai ya wallafa wani sakon Twitter inda ya ce galibin masu dauke da cutar korona a jihar almajirai ne da gwamnatin Kano ta koma da su Kaduna.

Hasalima a sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar 4 ga watan Mayu, ya ce a cikin mutum 72 da suka kamu da cutar a ranar, "kashi 65 almajirai ne da aka dawo da su daga jihar Kano."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba da gangan take mayar da almajiran jihohinsu na asali ba.

Wata sanarwa da Malam Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje ya aike wa manema labarai ranar Lahadi, ta ce dukkanin gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince su mayar da almajirai jihohinsu na asali kafin su dauki wannan matakin.

"Mun amince a wurin taron Kungiyar Gwamnonin Arewa cewa kowacce jiha ta mayar da almajirai jihohinsu na asali. Shi ya sa muke kai su jihohinsu da kyakkyawar niyya da kuma tsari, dukkan almajiran da ba 'yan Kano ba ne muna kai su jihohinsu na asali," a cewar Malam Anwar.

Ya kara da cewa bai kamata a rika mayar da batun siyasa ba.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa: "Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka mu ma ake dawo mana da almajirai 'yan asalin jihar Kano daga wasu jihohin.

''Don mu ba ma yin surutu a kan batun ba ya nufin dukkansu lafiyarsu kalau ba sa dauke da COVID-19." in ji Ganduje.

Gwamnan na Kano ya tabbatar da cewa wasu daga cikin almajiran da aka koma da su Kano suna dauke cutar korona, yana mai cewa "amma mu ba mu mayar da batun siyasa ba. Saboda mun yi amannar cewa ba surutu muke bukata ko neman suna ba. Abin da suke bukata a wannan mawuyacin hali shi ne kulawa."

Masana harkokin lafiya a Najeriya sun sha garagadi da jan kunnen mahukunta da su daina amfani da siyasa a yakin da suke yi da cutar korona, domin kuwa hakan zai sa mutane su ci gaba da mutuwa yayin da 'yan siyasa suke ce-ce-ku-ce da juna kan matakan da suka dace don dakile cutar.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus