Coronavirus: 'Mayar da almajirai garuruwansu bai dace ba'

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya masana sun soma tsokaci kan matakin da gwamnatocin jihohin arewacin kasar 19 suka dauka na rufe dukkanin makarantun tsangaya da nufin shawo kan cutar korona a yankin.
Kididdiga dai ta nuna akwai almajirai miliyan tara a yankin arewacin Najeriya, abin da ya sa ake fargabar yaran ka iya yada cutar ta korona idan har wasu daga cikinsu sun kamu da ita.
Za a iya cewa wannan ne karon farko da gwamnatocin jihohin arewacin Najeriyar ke kokarin kwashe almajiran da ke jihohinsu zuwa jihohinsu na asali.
Wannan mataki dai a ganin wasu kwararru kan cututtuka masu yaduwa bai dai-dai bane kamar yadda Dakta Nasiru Sani Gworzo, kwararre kan cututtuka masu yaduwa a Najeriya ya shaida wa BBC.

Dakta Nasir, ya ce " Abu na farko idan aka kalli yanayin da ake ciki a yanzu yanayi ne mai hadari, don haka daukar mutane masu yawa a fita da su zuwa wani gari akwai hadari".
Kwararren ya ce " Ta yiwu a cikin almajiran da aka kwasa tun da a mota daya aka saka su wani ko wasu daga cikinsu na dauke da cutar korona don haka za su iya zuwa su yada ta a inda za a kai su watakila ma a garin nasu ba bu mai cutar".
Ya ce " Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, domin ga duk wanda ya san sirrin makarantun tsangaya wuri ne da ke da cunkoson almajirai suke kuma kwana tare, don haka idan aka yi rashin dace mutum daya ya kamu da cutar to sai ta Allah a wannan makaranta".
Dakta Nasir ya ce, yakamata a wajen mayar da almajiran garurunwansu na asali to abi ka'idojin da suka dace kamar na nisantar juna, idan za a dauke su a mota to kada a cunkusa su waje guda a bayar da tazara.
Kwararren ya ce baya ga bayar da tazara a wajen daukarsu a mota, to yakamata a kula da tsaftarsu kamar wanke hannu, sannan kuma a basu man goge hannu, kuma idan da hali ma a basu takunkumin rufe fuska domin kada wani ya shaki numfashin wani a cikin mota.
Dakta Nasir Sani Gwarzo ya ce, " Idan har da hali koda yake abune mai wuya da an rinka yi wa almajirai gwaji"
Ya ce amma a gaskiya abu mafi kyau gara a mayar da su gidajensu tunda duk makarantu na boko ma an rufe da sauran wurare.
Daktan Nasir ya ce, yin hakan ba laifi don zai taimaka wajen rage yaduwar cutar da kuma rage cunkoso a makarantun allo kuma suma almajiran an musu gata.

Matashiya
Gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar 19 dai sun sanar da rufe dukkannin makarantun tsangaya da zummar shawo kan annobar korona a yankin.
Akalla yara miliyan tara ne aka yi hasashen za a mayar da su gaban iyayensu sakamakon annobar.
Iyaye da yawa a arewacin Najeriya na tura yaransu zuwa makarantun allo domin samun karatun Al Kur'ani mai tsarki, wadanda suka hada da kananan yara 'yan kasa da shekara shida.
Ana bayyana damuwa kan makomar yaran, musamman yanzu da cutar korona ke ci gaba da bazuwa a jihohin arewancin Najeriya.
Wannan ne ya sa gwamnonin arewa suka yanke shawarar tura almajiran zuwa garuruwansu na asali daga cikin matakan da suke dauka na dakile bazuwar cutar a yankin.










